Menu

Ko Barcelona za ta lashe La Liga na bana kuwa?

 118449239 Gettyimages 1204561500 Lionel Messi, kyaftin Barcelona

Tue, 11 May 2021 Source: BBC

Saura wasa uku-uku suka rage a karkare kakar La Liga ta bana, bayan da Atletico ce ta daya a teburi sai Real ta biyu, yayin da Barcelona ke mataki na uku.

A bara Barcelona ta kasa lashe kofi a dukkan fafatawar da ta yi. amma a bana ta yi nasarar cin Copa del Rey, amma tana fuskantar kalubale a La Liga.

A kakar La Liga ta bana, Barcelona ta barar da maki da yawa a Camp Nou, filin da a baya duk wata kungiya ke fargabar zuwa buga tamaula.

Ranar Asabar Barcelona ta samu damar hawa kan teburin La Liga, amma sai ta tashi ba ci tsakaninta da Atletico Madrid, hakan ya sa ta ci gaba da zama ta uku a teburin.

A kakar 2020/21 Barcelona ta kasa doke abokan hamayyarta Real Madrid da Atletico Madrid ta kuma bari wasu kananan kungiyoyi sun yi nasara a kanta.

Cikin tsakiyar gasar La Ligar nan ba wanda ya bai wa Barcelona damar cewar za a yi takarar lashe kofin na bana da ita, daga baya ta sa kokarin da ya kai ta wannan matakin.

Kamar yadda kungiyoyi ke fama da rashin 'yan kallo a lokacin wasa, haka shima filin Camp Nou ke fama da rashin magoya baya da za su karawa kungiyar kwarin gwiwa.

Barcelona ta sha kashi a gida a hannun Real Madrid da ci 3-1 ta kuma yi canjaras da Sevilla da rashin nasara a hannun Granada da ci 2-1.

Wadan nan wasannin na daga cikin wadan da suka sa kungiyar ta ci karo da koma baya a kwanan nan da tuni ita ce ke ta daya a gasar La Liga ta bana.

Filin Camp Nou ya dai na bai wa kungiyoyi tsoro, inda Barcelona ta sha kashi da 3-0 a hannun Juventus a gasar Champions League, bayan da Barca ta ci wasan farko a Turin.

Haka kuma ba za a manta da cin da Paris St Geramin ta yi wa Barcelona a Spaniya ba, da ta kai yi ban kwana da gasar Zakarun Turai a hannun kungiyar Faransa.

Kawo yanzu Atletico Madrid ce ta daya a kan teburi mai maki 77, sai Real Madrid da maki 75, iri daya da na Barcelona da kuma Sevilla mai tazarar maki hudu tsakaninta da Real da kuma Barca.

Ranar Talata 11 ga watan Mayu, Barcelona za ta ziyarci Levante a karawar mako na 36, sannan ta karbi bakuncin Celta Vigo a karawar mako na 37.

Barcelona za ta buga wasan mako na karshe na 38 ranar 23 ga watan Mayu a gidan Eibar.

Abin tambaya ko Barcelona za ta iya lashe dukkan wasa ukun da suka rage mata? idan ta lashe wasannin ya makomar na Atletico Madrid da Real Madrid su kuma.

Saboda haka sai dai idan Barcelona tana da babban rabo shi ne kadai zai sa ta ci La Liga na bana kuma na 27 Jumulla.

Barcelona ce ta lashe kofin La Liga na kakar 2018/19, sai Real Madrid ta lashe na 2019/20.

Source: BBC