Menu

Ko Tinubu ya fara yakin neman zaben 2023 daga Jihar Kano ne?

 117746664 Tn Asiwaju Tinubu tare da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Mon, 29 Mar 2021 Source: BBC

Masana harkokin siyasa a Najeriya sun fara tsokaci kan bikin zagayowar ranar haihuwar Sanata Ahmad Bola Tinubu, jigo a jam'iyyar APC mai mulki da za a yi a Jihar Kanon Najeriya.

Wannan ne karon farko da ake yin bikin a wata jiha da ke arewacin Najeriyar, inda a baya an fi yin bikin a mahaifar Tinubu wato Legas.

Gabanin taron, Tinubu ya kai ziyara tare da duba wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin Kano ta yi, sannan ya gana da ƙabilun yankin kudancin kasar mazauna Kano da kuma wasu daga cikin malaman addinin Musulunci.

Kafin zuwansa Kano, Tinubu ya je Jihar Katsina a makon da ya gabata, har ma ya bai wa 'ƴan kasuwar da gobarar babbar kasuwar jihar ta shafa tallafi.

A na sa ran manyan ƴan siyasa daga jam'iyyar APC da masu riƙe da muƙamai daga sassan ƙasar daban-daban za su je Kano don halartar wannan biki.

Sai dai mai bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa rashin kyawun yanayi ya hana wasu manyan ƙasar da dama tafiya Kanon.

Ya ce: "Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Asinbajo, da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila da ni kaina ba za mu samu damar halartar taron ba, sakamakon rashin kyawun yanayi da ake fama da shi a Kanon, dalilin da ya hana tashi da saukar jiragen sama."

Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa ne a kwalejin share fagen shiga jami'a ta CAS a Kano, yana da ra'ayin cewa lallai da walakin goro a miya.

A cewarsa: ''Bisa al'ada a birnin Lagos ake yin bikin, amma abin mamaki bana an kawo shi arewacin Najeriya kuma a Jihar Kano, wannan ya nuna tabbas akwai alaƙa ta manufar Tinubu ta yada manufar siyasarsa a shekarar 2023, a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC mai mulki''.

Ƴan adawa ke yaɗa jita-jitar ɓaraka tsakanin Buhari da Tinubu - Fadar Shugaban Ƙasa

Kabiru Sufi ya ce tuni an samu masu sukar matakin, wadanda suke ganin a baya-bayan nan da aka yi ta samun tashin hankali a yankin Yarabawa Tinubu bai ce komai ba, alhalin yana daga cikin masu karfin fada-a-ji a yankin nasu.

"Wannan ya nuna lallai akwai siyasa a lamarin, kuma ana ganin zabar arewa da ya yi ba lallai 'yan arewa su yi murna da shi ba.

"To amma wasu na ganin an fito da muhimmancin Jihar Kano a siyasar arewacin Najeriya, tun da har Tinubu ya zabe ta a matsayin inda zai fara kada gogen share fagen siyasar 2023," in ji Sufi.

Masu lura da al'amuran yau da kullum ba su yi mamakin goron gayyatar da aka bai wa Tinubu zuwa Kano ba, ganin cewa da ma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na goyon bayansa, sannan ba za a gane tasirin taron ta nasara ko akasin haka ba sai an kammala shi da kuma abin da ya biyo bayansa.

Malam Kabiru Sufi ya ce ziyarar da Tinubu ke kai wa jihohin arewacin kasar duk na daga cikin zawarcin kuri'u na al'ummar yankin.

Mene ne alfanu da nakasun wannan ziyara ga jam'iyyar APC?

"Hakan zai iya zama alfanu ko naƙasu ga ita jam'iyyar APC, musamman idan jam'iyyun adawa suka tsaya tsaf suka dubi al'amarin suka yi wani shiri da zai ba su riba, sabanin wanda APC ta fara yi a yanzu, to zai iya zama nakasu a gare ta," in ji Kabiru Sufi.

"Amma idan fara shirin da suka yi da wuri bai sa jam'iyyun adawa sun farga sun fara nasu shirin ba, to APC za ta ci nasara da gajiyar wannan taro da na murnar zagayowar ranar haihuwar shi Bola Ahmad Tinubu a jihar Kano.

"Amma su kansu jam'iyyun adawar za su iya amfani da damar da suke da ita, idan aka yi la'akari da rarrabuwar kawuna da barakar da ke cikin jam'iyyar APC, za su iya cin gajiyar hakan,'' in ji Kabiru Sufi.

Me 'ƴan Najeriya ke cewa kan cikar Tinubu shekara 69?

Tun da sanyin safiyar Litinin shafin sada zumunta na Twitter ya ɗau batun cikar Bola Tinubu shekara 69 a duniya.

An ƙaddamar da maudu'i mai taken #Jagaban da kuma #TinubuIsKey ake ta amfani da su wajen taya shi murnar kai wa wadannan shekaru.

Wasu sun yi ta kuranta wasu kuma suna amfani da damar wajen sukarsa.

Yawancin saƙonnin da mutane ke wallafawa a shafin suna nuni ne da cewa suna fatan shi ne zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023, kuma suna maraba da hakan.

Amma a hannu guda akwai masu rajin cewa bai kamata matasa su zaƙe wajen assasa batun tsayar da Tinubu takara a shkearar 2023 ba, inda suke cewa lokaci ya zo da ya kamata a bai wa matasa dama su karbi ragamar mulkin.

Ga dai abin da wasu ke cewa:

Happy super birthday to the Asiwaju of Lagos, the Jagaban of Lagos, the political juggernaut of the West; the national leader of the All Progressives Congress, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Live long, sir!

Source: BBC