Menu

Koriya Ta Kudu: Matan da ke cikin tsananin talauci a ?asar da ke da matu?ar arzi?i

 116617450 Koreanelderly1.png Koriya Ta Kudu: Matan da ke cikin tsananin talauci a

Mon, 8 Feb 2021 Source: BBC

"Ta ya za ka iya rayuwa alhali bab abin da kake jira daga albashi sai albashi? Kalaman Cho Kyung-suk kenan mai shekara 82 da ke zaune a wani karamin daki da yake fayau.

Koriya Ta Kudu na daga cikin kasashen da ke da arziki a nahiyar Asiya, amma kusan rabin al'ummarta da suka haura shekara 65 na rayuwa ne cikin talauci, kamar yadda binciken kungiyar da ke fafutukar inganta tattallin arziki da hadin kan al'umma ta OECD na 2016 ya nuna.

Kuma wannan batu ne ya yi tasiri kan rayuwar mata a kasar, kamar yadda labarin Cho ya nuna.

Bugu da kari, rashin daidaito da kuma nuna bambancin jinsi ya ta'azzara lamarin.

Shinkafa da madara

Duk da tsufa da yake damunta, Chao na rayuwa ne cikin talauci, kuma yanayin yadda take lalurorin yau da kullum a gidanta ga alama ba abu ne da zai dore ba.

A lokacin da ta haura shekara 70 ta taba karbar hayar daki amma ba ta iya biyan haya, don haka ta nemi mai gidan hayar da ya yafe mata bashin da yake binta saboda ba ta da halin biya.

''Yar da nake da ita kwaya daya tilo ba ta da halin da za ta dauki nauyina," a cewar Cho.

Kuma rashin wata madafa baya ga dan tallafin da gwamnati ke ba ta na zamanta mai karbar fansho, Chao ta samu kanta a wani yanayi da ba za ta iya ciyar da kanta bayan ta biya kudin haya da sauran ababe kamar kudin wuta da na ruwa.

"A kowane wata kudin da ke shigo ni dakyar yake isa in sayi shinkafa da madara,'' a tabakin Cho.

Tsohuwar malama

Sai dai an yi lokacin da Cho ke shanawa.Ta shafe shekaru 10 a matsayin malamar makaranta, a wata firamare mai zaman kanta ta farko a Koriya Ta Kudu.

A lokacin albashinta ya kai akalla dala 900. "Abu ne mai wahala ka ga mace na karatu mai zurfi a lokacin, amma ni kam mahaifina ya taimake ni sosai,'' a cewar Cho.

To sai dai kamar mata sa'o'inta a Koriya Ta Kudu, Cho ta ajiye aiki ta yi aure inda daga nan ta fara dogara da aikin mijinta.

Kuma bayan ?am shekaru sai aurenta ya mutu.

Shekaru 40 da suka gabata sakin aure ya yawaita a Koriya Ta Kudu, duk da cewa ya ragu a shekaru ta 2000.

''Na gigita sa'adda aurena ya mutu kwatsam ba zato ba tsammani.Na rasa inda zan tsuguna dole ta sa rika aiki tukuru don na samu kudi.''

Rashin miji ba karamin tashin hankali bane acewar Cho.

''Na kasa samun abin da na sa rai cewa zai isheni lalura ga kuma reno da na ke yi.''

Kuma ganin cewa ga lalurorinta ga na ?arta, dole ta sa Cho ta nemi aikin wucin gadi kamar karantarwa da tsaron shago.

Sai dai kuma tana da shekaru 67 wani bala'i ya koma fada mata, a lokacin da ta samu ciwon shanyewar bangaren jiki, wanda hakan na nufin ba za ta iya aiki ba kamar da.

''Abokan aiki na ne suka fahimci me ya faru dani a dakina.Abunda kawai zan iya tunawa shine kwalliya nake yi a lokacin.''

Duk da Cho ta warke a lokacin da kai shekara 70, to amma fa dan abind aya rage daga kasonta na fansho bai taka kara ya karya ba.

Tsarin fansho

Tsarin fansho da Koriya Ta Kudu ke amfani dashi an kirkire shi ne a shekarar 1988, kuma yana samar da tallafi ne ga wadanda suka yi ritaya daga aikin gwamnati.

La'akari da cewa ana lissafa fanshon ma'aikaci ne dai dai da abinda ke shigo shi a wata, matan da ba sa karbar albashin kirki ko kuma suka ajiye aikin ba tare da sun kai wani matsayi ba, za ka ga cewa idan sun yi ritaya tallafin da suke samu cikin cokali ne.

Wata hanyar samun tallafin itace agajin da ake baiwa talakawa da ba su da cin yau balle na gobe kamar Cho.

A wannan tsarin ne kashi 70 na talakawan kasar da suka kai shekaru 65 zuwa sama suke.

Kowane talaka na samun dala 234 a duk karshen wata, to amma ba kudi ba ne da zai ishi mutun kawar da lalurorinsa ba kafin lokacin karbar wani tallafin.

Al'ummar Koriya Ta Kudu da ke shirin ritaya bayan da suka haura shekara 50 sun lissafa cewa suna bukatar dala 1,073 domin gudanar da lalurorinsu na yau da kullum a kowane wata.

Ga dadi ga wahala

Duk da matsin da take fuskanta, Cho ta samu sarari, bayan da gwamnati ta tallafa mata da wasu kudade da idan aka hada da abinda ta tara daga kudin da ake cire mata na mallakar gida sun kai kusan dala 43,000.

Hakan ya sa Cho ta samu kanta cikin sa'ida, ganin cewa za ta iya mallakar gida cikin dan lokaci.

To amma da dama tsofaffi a Koriya Ta Kudu ba su samu sa'ar da Cho ta samu ba, wanda hakan na nufin za su cigaba da zama babu muhalli.

Seo Jung-hwa itace shugabar cibiyar da ke taimakawa mata da basu da matsuguni da inda za su zauna a Seoul, kuma ta shafe shekaru 17 tana bada irin wannan taimako, da ya hada da wurin kwana da abinci da kuma taimakawa gajiyayyun su samu wani aikin.

Binciken da gwamnatin ta yi a 2019 ya nuna cewa daga cikin sama da mutun 3,000 da ba su da gidan kansu a Seoul, 1 daga 5 mata ne.

''Rabuwar iyali shi yake sa ake samun yawaitar marasa gidan zama a mafi yawan lokuta a Seoul,'' a cewar Seo Jung-hwa.

Daya daga cikin tsofaffin da ta ke taimakawa a cibiyarta itace Ahn Ok-rhan.

A cewar Ahn Ok-rhan ''karshen kaskancin da na fuskanta shine kwana a kan simintin bandakin tashar Seoul, kuma hakan yasa na fuskanci cin zarafi a lokuta da dama saboda gararamba a kan titi.''

Ahn ta shafe shekaru 20 ba ta da gidan kanta, bayan da ta guje wa abokn zamanta da ke cin zarafinta.

A lokacin ne kuma ta hadu da cutar tabin hankali. To amma da taimakon wannan cibiya a hankali ta warke har ma ta cigaba da karatunta, har ma ta smau aikin a wannan cibiya ta kuma tara dala 25,000 wanda ba kasafai ake samun wadda ta yi irin wannan sa'a ba.

Kuma bayan wasu yan shekaru ta mallaki gida tare da tallafin gwamnati.

''Ina farin ciki sosai ganin cewa ina iya kawata dakina yadda nake so.Na ma siyo kayan bacci yan kwanakin da suka wuce,Na kuma yi bacci cikin farin ciki da annashawa.'' A tabakin Ahn.

Tsawon rai babu abin lalura

Da farko dai mata sun fi maza tsawon rai kuma duk da haka ba su samu damar da mazan ke samu kan abinda ya shafi tallafi da sauran nasarorin rayuwa.

''Mata sunfi maza tsawon rai da kamar shekaru goma, kuma su suke daukar nauyin kansu bayan mazajensu sun mutu, a cewar Woo Jae-ryong na kungiyar RRC da ke bincike kan ritaya a Koriya Ta Kudu.

Ya kara da cewa ''mata da yawa na ajiye aiki saboda haihuwa ko reno, saboda haka ba sa samun damar aiki har lokacin da yakamata su yi ritaya kamar yadda maza ke yi.

Duk da abubuwa sun sauya, har yanzu kashi 56 ne mata a Koriya Ta Kudu ke aiki, kuma suna samun kashi 63 ne kawai na abinda maza ke samu.

Sauyin zamani

A al'adance ?a?a ne ke takalihun iyayensu lokacin da tsufa ya kama su a Koriya Ta Kudu, to amma zamani yasa abubuwa sun fara sauya wa.

A cewar mai sharhi Woo Jae-ryong bincike ya nuna cewa an samu sauyin da yasa a yanzu tsofaffi na shiga matsala kasancewar su ke kula da kansu.

Kuma lura da yadda tsofaffi ke shiga kangin talauci a Koriya Ta Kudun yasa ake fargabar abubuwa su dadacakude musu, ga kuma yawansu sai karuwa yake yi.

Kazalika ana saran ta zamo kasar da aka fi fuskantar yawan tsofaffi matalauta a yankin Asiya.

Kuma irin yadda hukumomi a Koriya Ta Kudun suka zabi su tunkari wannan matsala da tsofaffin kasar ke ciki zai bayyana makomarsu a shekaru masu zuwa.

Source: BBC