Ku latsa hoton da ke sama don kallon cikakkiyar hira da malamar:
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya yi hira ne da Dokta Maryam Abubakar Abba, wata malamar addinin Musulunci a Sudan amma ƴar asalin Najeriya.
Malamar ta ce karatu ne ya kai ta ƙasar Sudan inda ta fara tun daga matakin koyon Larabci kana daga bisani ta yi digirinta na farko, ta yi na biyu sannan a yanzu tana yin digirin-digirgir duk a Sudan.
Mahaifinta Malam Abubakar Abba ɗan asalin jihar Adamawa ne wanda aikin koyarwa ya kai shi Kano, inda a nan ya auri mahaifiyar Maryam.
An haifi Maryam a cikin birnin Kano kuma ta tashi a uguwar Yakasai. Kanwa ce ga tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, kuma shi ne ya kai ta SUdan don yin karatu.
Dokta Maryam ta ce tun tana ƙarama mahaifinta ya ci burin kai ta ƙasar Masar don ta yi karatu kan harshen Larabci. Ta fara karatu tun daga firamare har ta je sakandaren ƴan mata ta Larabci ta WATC Gwauron Dutse.
Bayan ta kammala aji uku sai ta koma makaratar Jahun inda ta kammala.
Daga nan ta fara karatu a Jami'ar Bayero ta Kano, amma a ta daɗe da farawa ba sai ta koma Sudan inda ta ci gaba da karatun digirinta a 1991.
Digirinta na farko ta yi ne a kan Larabci, na biyu da digirin-digirgir kum,a ta yi ne a kan koyar da waɗanda ba su iya Larabci ba.
A yanzu shekararta 30 a Sudan, amma ta kan je gida Najeriya don yin hutu.
Sannan ta yi hidimar ƙasa a Najeriya kuma ta yi aikin koyarwa.
Sannan Dokta Maryam ta fara gabatar da tafsiri tun a shekarar 1999, kuma ta kan gabatar da lakcoci da yin wa'azukka a gidajen rediyo.
Kazalika akwai shirin da ta dinga gabatarwa a gidan rediyon Kano na Rauda fir Riyadul Jannah. Sannan ta kan fassara hudubar Juma'a ta Masallacin Manzon Allah SAW kai tsaye ga masu sauraro a gidan rediyon.
Dokta Maryam ta kuma gabatar da wani shirin a gidan talbijin na jihar Kano ARTV mai taken Riyadus Saliheen, kuma har yanzu tana yinsa.
Malamar ta yi iya yaruka hudu Larabci da Hausa da Fillanci da Turanci. Dokta Maryam ta ce ba ta da burin yin abin da zai amfani al'umma.
"Babban jin daɗina shi ne yadda maigidana ya ba ni izinin yin karatu da ayyukan da'awa.
Malamar tana da aure da yara huɗu. Ta haɗu da mijin nata wanda ɗan Najeriya ne a Sudan.
Babban ɗanta yana karatun Injiniya sai ta biyun mai yi karatun haɗa magunguna ta ukun kuma tana karatun likitanci, sai ɗan autanta da yake sakandare.