Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira da Abdullahi Uwaisu Mohammad Abba:
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke birnin Kano a Najeriya, Sheikh Abdullahi Uwaisu Mohammad Abba, ya ce akwai bukatar kawo gyara a tsarin koyarwa a makarantun zaure saboda "rayuwa na kara fadada kuma mutane sun kara yawa."
Malamin ya bayyana hakan ne a cikin shirin Ku San Malamanku na BBC Hausa wanda yake tattaunawa da malaman addini kan rayuwarsu.
Ya ce matsalar da ake fuskanta ita ce yadda ake kafewa kan wani tsari guda daya ba tare da sauyawa ba - "sai a ce abu yadda yake jiya, dole haka za a tafiyar da shi a yau duk da a yau din an gamu da wasu matsaloli wadanda suke bukatar dole sai an sauya".
"Karatuttunka da ake yi na gaba daya kamar wanda kuka zo kuka samu sun fi dadin tafiyarwa saboda daman iyakantattun lokuta ne gyare su za a zauna misali wannan takwas zuwa tara an tashi," in ji Malamin.
Ya ce bai dace a ce malami ya wuce sa'a uku yana koyarwa bai huta ba "amma ka'ida sai a ce ana neman ka yi awa shida ko awa bakwai wanda dole idan ka fara, awa daya, awa biyu kana jin nishadi a kan koyarwa, amma awa uku, awa hudu to ka fara jin jiki ko kwakwalwar kanta tana bukatar a ce ta huta".
A cewarsa, bai taba himma wajen ilimi ba domin ya zamo wani abu a duniya - "babbar manufa a ce kawai na san ilimin".
Tarihin Sheikh Abdullahi Uwaisu
An haifi Sheikh Abdullahi Uwaisu a unguwar Limanci ta birnin Kano da ke Najeriya a shekarar 1954. Ya ce sai da ya fara karatun Ƙur'ani kuma bayan ya sauke ya fara hadda ne ya soma karatun litattafai ka'in-da-na'in.
Ya ce ya hada Karatun Qur'ani da na litattafai - "don akwai lokacin da ma saboda kokarin cewa ya zamo an dukufa ga karatun Litattafai ya zamo Qur'anin da sauri da sauri aka yi".
"Sai da ta kai a kullum sai na rubuta ribin hizibi (nisfi) kuma gobe na wanke na sake rubuta wani nisfin, shi yasa kusan duk sati sai na yi izu biyu da rabi," in ji shi.
Bayan nan ne kuma ya dukufa wajen karatun litattafai.
Ya ce ya fi sabo da ilimin nahawu kuma ya fi dauke masa hankali fiye da sauran ilimai.
"Tun da na taso ina sha'awar na ga yadda a zamanance ake karanta ilimin da ake karantawa a makarantu na soro," in ji malamin.
A wajen mahaifansa kadai ya yi karatu amma ya ce ya kan saurari yadda wasu malaman suke karantarwa.
Abin da ya fi faranta wa Malam rai
Sheikh Uwaisu ya ce yana jin dadi a duk lokacin da ya ji wani hangensa kan wani abu ya zo daidai da wasu manyan malaman na da.
Sannan "babban abin farin cikina shi ne a ce na dade ina neman littafi, musamman a ce na yi tafiya wata kasa na je wajen sayar da litattafai na ga ga littafin ya samu, sai na ji jikina yana makyarkyata saboda murna da samun (littafin)."
Ƙasashen da malam ya fi son zuwa
Sheikh Uwaisu ya ce kasashen da ya fi son zuwa su ne Mauritania da Morocco saboda wasu litattafai da dama da malaman kasar suka yi wadanda ba a buga su ba ko kuma "bugu ne da aka yi don yan kasar".
"Ina son a ce na je na samo irin wadan nan litattafan, yadda zan samu na zuana kamar wata biyu ko wata uku yadda zan kewaya na binciko abin da zan binciko a wajen". a cewar malamin.
Iyali
Malamin ya ce yana da mata biyu da 'ya'ya wadanda suke a raye sun kai bakwai sai jikoki kuma 15.
Ya kuma ce ba zai manta da mutuwar mahaifiyarsa ba da kuma yarsa da ta mutu wajen haihuwa saboda irin dimuwar da ya shiga a lokacin.
Malamin bai yi karatun zamani ba, amma dai ya ce ya ringa bibiyar manhajoji da ake amfani da su a makarantu na zamani, har ma yana taimaka wa wadanda suke karatu a irin wadancan makakarantun.
Duk da cewa bai yi ilimin zamani ba, Sheikh Abdullahi Uwais ƙwararre ne a ilimin lissafi da tattalin arziki da wasu fannonin na ilimin zamani.
Malamin ya kasance madogara da ake tuntuɓa daga jami'o'i kan wasu mas'aloli da suka shafi darussan addinin Musulunci da harshen Larabci.