Menu

Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdulwadud Harun Attijjaniy na Ghana

 117621410 P099chrm Sheikh Abdulwadud Harun Attijjaniy

Fri, 19 Mar 2021 Source: BBC

Shugaban gudanarwa na darikar Tijjaniyya a kasar Ghana Sheikh Abdulwadud Harun Attijjaniy, ya ce a Ghana akwai fahimtar juna tsakanin kungiyoyin Musulmin kasar, haka kuma suna zaman lafiya da mabiya wasu addinan.

Malamin ya fadi hakan ne a cikin shirinmu na Ku San Malamanku na wannan makon.

Ya bayyana cewa an haife shi a darikar Tijjaniyya ya kuma taso a cikinta, sannan ya yi rubuce-rubuce a kanta.

Ya ce a Ghana su babu ruwansu da bambancin aƙidu. "Muna da haɗin kai tsakanin ɗariku da shi'a da sunni duka," in ji shi.

Sheikh Harun ya ce ya shiga kauyuka da birane domin yada addinin Musulunci da darikar ta Tijjaniyya.

Wane ne Sheikh Abdulwadud Harun Attijjaniy?

An haife shi a unguwar Abuwabu da ke birnin Kumasi a ƙasar Ghana.

Ya fara karatu a hannun mahaifinsa daga baya ya koma karatun Al-ƙur'ani a hannun wani abokin mahaifinsa Malam Umar.

Ya yi sauran littattafai a hannun mahaifinsa.

"Na tashi a gidanmu na ga ana bin dariƙar tijjaniya kuma kan tarbiyyarta na tashi don tun muna yara ake tura mu Zawiyya har muka girma.

"Na yi yawo sosai wajen kira da karantar da ɗariƙar Tijjaniyya," in ji shi.

Ya ce yana da burin zama jagora a ɗarikar Tijjaniya na ƙasar Ghana wanda zai dinga jagorantar ayyukan ci gaban addini.

Yana da mata biyu da ƴaƴa biyar. Sannan ya ce a abinci duka ya fi son tuwo sai kuma doya.

Source: BBC