Menu

Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Nazifi Al-Karmawi

 118398431 Malamabdulwahid Sheikh Abdulwahid Muhammad Nazifi Al-ƙarmawi

Fri, 7 May 2021 Source: BBC

Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira da Abdulwahid Muhammad Nazifi Al-Karmawi:

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Abdulwahid Muhammad Nazifi Al-ƙarmawi ya ce yana yawan sanya maganar aure a karatunsa ne domin shi ne jigon rayuwar mutane.

Malamin ya bayyana hakan ne a cikin shirin Ku San Malamanku na BBC Hausa wanda yake tattaunawa da malaman addini kan rayuwarsu.

Malamin ya ce ta hanyar aure ne ake samun albarkar rayuwa baki ɗayanta, don haka idan aka yi karin bayani kan haƙƙin ma'aurata hakan zai taimaka wa ma'auratan su gane yadda za su samu aljannarsu.

"Abin da yasa muke yawaita magana aka haƙƙoƙi na aure akan miji da sauransu, ta nan ne ake samu ƴaƴaye masu albarka waɗanda Annabi zai yi alfahari da su," in ji Sheikh Nazifi.

Malamin ya ce yawan matsalolin aure da ake samu a tsakanin al'umma ya sa ya zama wajibi a mayar da hankali kan haƙƙoƙin aure da abin da yake tattare da su.

"Idan ba a samu damar kare haƙƙin miji ba shi kuma ya kiyaye na mata, to zama ba zai yi albarka ba a samu yadda ake so".

Muna sa nishadi a karatunmu don a fahimta

Ɗaya daga abin da Sheikh Nazifi Al-ƙarmawi ya shahara da shi shi ne barkwanci da nishaɗi a yayin karatu.

Da aka tambayi malamin ko me ya sa yake haka, sai ya ce tun daga inda aka fara koyar da su malamansu na saka nishaɗi wajen koyarwa.

Ya ce"Idan ka ga yadda muke yi da su Malam Babba (Mahaifinsa) za ka ɗauka mu jikokinsu ne, bayan kuwa mu ƴaƴa ne."

Shiekh Al-Ƙarmawi ya ce shi ma ya zabi saka nishaɗi a karatu ne a matsayin hanyar da zai ringa jina hankali a fahimci saƙon da yake son isarwa.

"Sanya nishadi a darusa zai bai wa wasu damar fahimtar karatu cikin sauƙi,"

Tarihin Sheikh Ƙarmawi

Sheikh Nazifi Al-ƙarmawi mutumin Kano ne shi, kuma an haife shi a cediyar 'yan gurasa, a ranar 15 ga watan Sha'aban Hijira 1387 wanda ya yi daidai da 2 ga watan Afrilu 1966."

Ya ce "Sunan mahaifina Sheikh Muhammad Awwal wanda aka fi sani da Shehu Malam ƙarami." Mahaifinsa ɗan uwan shahararren wani Malami ne da aka yi a Kano, Sheikh Atiku Sanka.

Asalinsu mutanen Masanawa ne a jihar Katsina, kuma jikokin babban malamin nan ne da ya rayu a Katsina, wanda aka fi sani da Wali Dan Masani.

Sheikh Nazifi ya fara karatu a hannun mahaifinsa kamar yadda mafi yawan malamai ke yi, don haka baki ɗaya karatun farko a gaban mahaifinsa ya yi.

Malam ya yi karatu a hannun malamai da dama a cikin garin Kano, wasu malaman mahaifinsa ne ya haɗa su da shi kamar su: Shehu Abdulmajid.

Yace ya yi karatu a hannun Babban almajirin mahaifinsa wanda kuma shi ne halifan farko na mahaifinsu, wato Shehu Malam Abubakar Yahaya wanda ake kira Malam Garba Cheɗiya.

"Malam ne ya tarbiyyantar da ni tarbiyya ta ruhi kuma ta ɗarika wanda gaskiya na yi karatu da wurinsa da dama," a cewar Sheikh Al-ƙarmawi.

Sheikh Nazifi Al-ƙarmawi ya ce a wajen Malam Garba Cheɗiya ya yi dukkan karatuttukan sufanci da litattafan ɗarikar Tijjaniyya tun daga ƙanana har zuwa manya, kamar Jawahirul Ma'ani da Rimahu.

"Akwai malamai da yawa da muka yi karatu a wurinsu na fannin hukunce-hukuncen addini da kuma harshen larabci da dai sauransu."

A bangaren karatun al-Kur'ani kuwa a wuri daya Malam sha duka a wurin babban yayansa, "cikin Suratu Mudassir, wajen da ake cewa Farrat min kasuwara, sai in rika cewa Farras min".

Ya ce ya yi haddar Alƙur'ani a hannun Sheikh Mukhtar Alaramma a makaratan Sheikh Manzo Arzai.

'Ina da mata biyuda ƴaƴa 14'

"Ina da mata biyu Hauwa da Bahijja, "Hauwa amanar mahaifiyata ce a wurina" Kan mahaifiyata ta rasu ta yi ta jaddada mani na riƙe mata Hauwa amana.

Kuma muna zaune da Hauwa kalau, da yara 10 tsakaninmu zamanmu sai san barka.

Tamkar yadda ya yabi uwar gidansa, Sheikh Nazif ya kuma yabi amayarsa Bahijja, wacce ya ce suna zaman lafiya da mutunta juna. Sannan ya ce duka matan na sa suna matuƙar taimaka masa.

Bahijja tana da ƴaƴa hudu tare da malamin.

Abincin da Malam ya fi so

Da aka tambayi malamin abincin da ya fi so sai ya ce, ba shi da wani takamaimen abinci domin kuwa komai yana ci.

To sai dai ya ce yana matuƙar son kunun tsamiya ko na gyaɗa, musamman ma idan akwai ƙosai mai zafi.

'Ya kamata a rika daukar mata ana zuwa shan iska'

Sheik Nazifi ya ce ya kamata ma'aurata su rika daukar iyalansu suna zuwa shan iska wuraren shaƙatawa.

Malamin ya ce a wasu lokutan ya kan je wasu ƙasashen don ya shaƙata, kuma duk lokacin da zai tafi ya kan tafi da iyalinsa su shaƙata tare.

"Na kan ɗauki matana mu tafi ƙasashe irin su Dubai, ai in ban tafi da su ba ya zama ina fadin abin da bana aikatawa," in ji Malam.

Hakan yana ƙara soyayya da danƙon zumunci tsakanin ma'aurata, "Irin shan iskar da na fada maka amma ba irin ta singa ba".

Source: BBC