Menu

Lafiya Zinariya: 'Yadda 'ya'yana takwas suka mutu a ciki'

 117620469 P09b67h2 Lafiya Zinariya wata shiri ne na BBC mei kula dalafiyan mata

Sat, 20 Mar 2021 Source: BBC

Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren shirin Lafiya Zinariya:

Wata mata mai suna Hadiza Mohammed ta bayyana wa BBC yadda ta haifi yara takwas dukkaninsu suka mutu a wajen haihuwa.

Ta ce likitoci ba su kai ga gano dalilin da yasa take wabi ba.

'Yadda nake dawainiya da ciki daga karshe kuma dan ya mutu, abin yana sosa mini rai' in ji Hadiza

Matar ta ce duk da cewa ta rungumi kaddara, sai dai bata fitar da rai ba.

Hukumar lafiya ta Burtaniya, NHS ta ce akalla ana samun mace daya da ke haihuwar jariri ba rai, a cikin haihuwa 200 da ake samu a kasar Ingila.

Inda ta kara da cewa ba ko da yaushe ake iya kaucewa mutuwar jarirai a ciki ba.

Amma akwai wasu hanyoyin da za a iya bi domin rage hadarin faruwar hakan.

Wasu daga cikin hanyoyin sun hada da kaucewa wasu daga cikin abubuwan da suke haddasa mace-macen. Wato mai ciki ta daina shan taba da giya da kuma shan miyagun kwayoyi.

Haka kuma ta dinga zuwa awon ciki, ta kuma kiyaye kamuwa da cututtukan da kan janyo wannan matsala.

Kuma a duk lokacin da ta ji ciwon ciki ko jini na fita ta gabanta ko kuma kaikayi, ta shaida wa ma'aikatan lafiya.

Sannan mai juna biyu ta dinga kula da motsin jaririnta.

Hakazalika, ta dinga kwanciya ta gefenta na dama ko hagu, maimakon kwanciya a rigingine.

Musamman idan ciki ya kai mako 28.

Mai ciki ta dinga cin abinci mai gina jiki tare da kiyaye wasu nau'ukan abinci da ka iya shafar lafiyar jaririnta.

Source: BBC