Menu

Lionel Messi: PSG na ci gaba da sa ido kan abunda ke faruwa a Barcelona

 118618194 F5762bde 5541 4af2 A530 45ab28bd2ceb Lionel Messi ne kyaftin din Barcelona

Mon, 24 May 2021 Source: BBC

Duk da cewa wasa daya ya rage a kare gasar La Liga ta bana, har yanzu babu batun kulla sabuwar yarjejeniya tsakanin Barcelona da Lionel Messi.

Rahotanni sun nuna cewa PSG na nan na ci gaba da sa ido kan yadda lamurra ke tafiya game da batun tsayawa ko kuma barin Messi Barcelona.

Kwantiragin Messi dan kasar Argentina mai shekaru 33 za ta kare ne a karshen kakar bana, kuma har yanzu babu wata magana a kasa game da makomarsa a kungiyar.

Masana kwallon kafa a Sfaniya kamar su Guillem Balague na da ra'ayin cewa ''Lionel Messi ba zai yi gaggawar yanke hukuncin ci gaba da zama a Barcelona ba daga nan har zuwa mako biyu.''A cewar Balague.

A bara ne dan wasan ya aike da sakon bukatar barin kungiyar a lokacin da ta fada cikin mummunan yanayi na rashin nasara.

To amma yarjejeniyar da aka kulla da shi a baya ta nuna cewa ba zai iya barin kungiyar ba har sai an biya Yuro miliyan 700, matsawar aka wuce 10 ga watan Yuni 2020 bai bayyana cewa yana so ya bar kungiyar ba.

Hakan yasa dole ya zauna a Barcelona, lura da cewa babu kungiyar da za ta biya wannan kudi don daukar sa.

Mai horar da Barcelona Ronald Koeman ya ce yana fatan Messi bai buga wasansa na karshe ba a makon da ya gabata, a wasan da suka yi rashin nasara har gida a hannun Celta Vigo.

Yanzu haka Messi na hutu kuma ba zai buga wasan karshe ba da kungiyarsa za ta yi a gidan Eibar.

Kuma ganin cewa ba shi da wata yarjejeniya da Barcelona yasa masana ke hasashen cewa da wahala ya cigaba da zama, a daidai lokacin da manyan kungiyoyi kamar PSG ke zawarcinsa ba.

Wasu jaridu sun ba da rahotannin cewa tuni Barcelona ta fara duba yiwuwar kawo abokin Lionel Messi wato Sergio Aguero, wanda zai bar Manchester City a karshen kaka.

Source: BBC