Menu

Littafin rayuwar Aisha Buhari na "Ta Daban" ya ja hankalin ƴan Najeriya

 117886923 Mediaitem117886922 Uwargidan shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari

Sat, 10 Apr 2021 Source: BBC

Uwargidan shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari na ta shan yabo da suka a shafukan sada zumunta da muhawara bayan ƙaddamar da wani littaffi da aka yi mai ɗauke da tarihin rayuwarta.

A ranar Alhamis ne aka ƙaddamar da littafin mai taken "Aisha Buhari, Being Different", wato "Aisha Buhari, Ta Daban," wanda babbar mai taimaka wa shugaban ƙasaa ta musamman kan harkokin mata Dr. Hajo Sani ta wallafa.

Wata sanarwa da mai taimaka wa uwargidan shugaban ƙasar kan yaɗa labarai Aliyu Abdullahi ya fitar ta ce, Dr Hajo ta yi littafin ne domin girmama Hajiya Aisha Buhari.

An yi taron ƙaddamarwar a fadar shugaban ƙasa da ake Abuja, babban birnin Najeriya, a daidai lokacin da Shugaba Buharin yake Landan don ganin likita.

Sai dai shugaban Ma'aikatan Fada Shugaban Ƙasar Farfesa Ibrahim Gambari ya wakilci Shugaba Buhari. Kana sauran manyan baƙin da suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo da matarsa Dolapo da jagoran jam'iyya mai mulki ta APC Asiwaju Bola Tinubu.

A shafin Tuwita sunan Aisha Buhari na daga cikin waɗanda suka fi tashe a ranar Alhamis saboda littafin.

Me halarta taron suka ce?

Jagoran jam'iyya mai mulki ta APC Asiwaju Bola Tinubu ya ce tunanin da wasu mutane ke yi cewa ofishin matar shugaban ƙasa ba shi da amfani ba zai taɓa tasiri ba, saboda rawar da Aisha Buhari ke takawa ta kore batun nasu.

Tinubu wanda shi ne shugaban taron ƙaddamar da littafin ya ce: "Babu wanda zai iya sake ƙalubalantar rawar da matar shugaban ƙasa ke takawa.

"A baya akwai masu kushe ofishin matar shugaban ƙasa da cewa ba ya cikin kundin tsarin mulki. A yanzu dole su haƙura su bar wannan zancen saboda rawar da Asiha Buhari ta taka."

Jagaban ya ƙara da cewa Aisha Buhari ta kasance wata ginshiƙi ba ga shugaban ƙasa ba kawai, har ma ga ƴan Najeriya waɗanda ita da mijinta ke jagoranta cikin kishin ƙasa.

Shi ma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya bayyana uwargidan shugaban ƙasar da cewa ita murya ce ta wadanda ba su da murya.

Gwamnan wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya ya ce rashin ƙumbiya-ƙumbiyar Aisha Buhari ya sa ta zama abar ƙauna ga ƴan Najeriya.

"Ko da yake wasu za su kalli halayyarta ta tsage gaskiya a matsayin rashin dattaku, amma gwamnoni na alfahari da yin mu'amala da ita a matsayinta na mai kare marar ƙarfi," in ji shi da yake magana a madadin gwamnonin ƙasar.

An ƙaddamar da wannan littafi ne na Aisha Buhari bayan mako uku da komawarta Najeriya daga Dubai, inda ta shafe kusan wata shida a can tana jinya kamar yadda wasu rahotanni suka ce.

Source: BBC