Menu

Ma'aurata mabiya Hindu da Musulmi na cikin tsaka mai wuya a Indiya

 117512905 Gettyimages 1229888208 Sabuwar doka ya haramta soyyaya tsakanin mabambantan addinai

Tue, 16 Mar 2021 Source: BBC

Wata sabuwar doka mai cike da cece-kuce da ke haramta soyayya tsakanin mabambantan addinai ya jefa ma'aurata mabiya addini na Hindu da Musulmi cikin tsaka mai wuya.

Lamarin ya harzuka ƙasar Indiya baki ɗaya, ba iyalai kaɗai ba.

Wannan yanayi ya jefa rayuwar ma'aurata da masoya da dama cikin hali da ƙaƙa-ni-ƙayi.

Ayesha da Saurayinta, Santosh (waɗanda aka sakaya sunansu) sun tsere."Iyaye na sun zo nema na yanzu haka suna zagaye," a cewar Ayesha."Muna cikin fargaba. An ba mu shawarar mu zauna a cikin gida."

Ma'auratan, masu shekara 29, sun tsere daga gidansu da ke yammacin jihar Gujarat. Yanzu haka, suna killace a wani gida - bene mai hawa biyu - a Delhi.

Akwai kuma wasu ma'aurata su ma da suka ɓuya tare amma su sun fito ne daga jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya.

A Nuwamban 2020, Uttar Pradesh ta kasance jiha ta farko da ta amince da dokar haramta tilasta wa mutum yin addini - ma'ana haramcin tilasta "sauya addini" ta karfi ko yaudara da sunan aure.

Wannan martani ne kan abin da ƙungiyar masu tsautsaura ra'ayi na addinin Hindu suka kira "jihadin soyayya", kalmar nuna ƙyama da ke tunzara zarge-zarge marasa tushe kan maza Musulmi da ake ganin suna soyayya da matan Hindu da nufin Musuluntar da su bisa sharaɗin aure.

Dokar ta kai ga tilasta kama mutane da dama da karɓan korafe-korafe a Uttar Pradesh, jihar da jam'iyyar kishin addinin Hindu wato BJP ke shugabanci.

An kuma fitar da makamanciyar wannan doka a jihar Madhya Pradesh da ita ma BJP ke mulki, da kuma Gujarat, da yanzu haka ke ƙoƙarin aiwatar da irin haka.

Don haka yanzu masoya na tsere wa daga jihohin uku zuwa yankunan da suke ganin za su tsira kamar Delhi.

Ma'aurata da ke da mabambanta addini ana yi musu rajista ƙarƙashi tsari na musamman na dokar aure, wanda ake kwashe kwanaki 30. Sai dai suna kasancewa cikin fargaba da zullumi a tsawon kwanaki na yiwuwar kai musu hari, musamman da sabuwar dokar da ke haramci kan irin wannan aure.

Wannan yanayi na sake zama babban ƙalubale ga Ayesha da Santosh da suka shafe shekara 13 suna soyayya.

Sun hadu a kwaleji a Gujarat a 2009. Yana karatu a Gujarati, ɗalibin ne da ke nazartar tattalin arziki.

"Muna haɗuwa a aji guda," a cewar Ayesha. Sun zama abokai har suka girma tare. Bayan shekara biyu, ta fuskance shi domin sanin ko yana son ta, kuma ya amsa cewa eh yana son ta, me zai hana shi faɗin abin da ke ransa?

Santosh yana matukar ƙaunarta amma kuma yasan cewa akwai jan aiki a gabansu a Gujarat, jihar da ake fama da rikicin ƙabilanci.

Dukkaninsu sun fito daga iyalai masu rufin asiri a Indiya - Mahaifin Ayesha na ɗan ƙaramin sana'a kuma malamin makaranta ne.

Mahaifin Santosh akawu ne a jami'a, inda aikinsa shi ne shigar da bayanan ɗalibai a na'ura. Sannan yana sana'ar daukan hoto.

Ayesha Musulma ce, shi kuma Santosh ƙabilar Dalit ne.

Suna iya tuna abin da ya faru a shekarar 2002, lokacin da aka kashe sama da Musulmi 1,000 a rikicin da ya biyo bayan tashin gobara a jirgin kasa, ƴan Hindu 60 suka mutu a Gujarat. An zargi Musulmi da haddasa gobarar. Wannan ya kasance ɗaya daga cikin rikici mafi muni na addini a Indiya.

Ayesha da Santosh, da suka girma tare cikin soyayya, suna sane da babban ƙalubale da taskun da soyayyarsu zata iya jefa su.

"A Gujarat, ya kasance masoya masu mabambanta addini babban matsala ne," a cewar Santosh."Ba zaku iya haduwa ba, babu yi wa juna magana, babu wani abin da zaku iya."

Bayan kammala makaranta a 2012, ba kasafai suke haduwa ba - idan kuma za su hadu to sai an shirya dabaru. Za su hadu a inda mutane ke taruwa saboda kar a zarge su. Kuma za su takaita ganawarsu.

"Zamu hadu fuskokinmu rufe da gyale," a cewar Santosh.

Suna dagewa wajen tattaunawa kan waya a koda yaushe.

"Mun adana lambar juna a waya da sunan boge ko kuma idan zamu yi magana ta wayar wasu," a cewarsa. Tun da iyayyen Ayesha na sa ido kan wayoyinta, Santosh wani lokaci na ƙwaiƙwayon muryar mata idan ya kira.

Lokacin da iyayyen Santosh suka gane suna soyayya, sai suka yanke shawarar yi masa aure. Sun tilasta yi masa baiko da wata yarinya a Nuwamban bara.

"Na shiga damuwa na tsawon kwanaki. Na kasa magana da Ayesha saboda ita ma a wannan lokaci iyayyenta sun fahimci muna tare," a cewarsa.

Mahaifin Ayeesha da ɗan uwanta na matsin lambar lallai ta yi aure.

Don haka Santosh da Ayesha sun yanke shawarar a ɗaura musu aure a Gujurat - sun shigar da korafin domin yin rajistar aurensu karkashin tsarin aure na musamman. Amma akawun kotun, wanda ya ga sunan Ayesha a takardunta, ya sanar da mahaifinta.

Santosh sun biya lauya dala 340 domin yi musu rajistar aure, amma lauyan ya ƙi.

"Babu wani jami'i da ya amince ya taimaka. Babu lauyan da ya amince ya karbi ƙorafinsu. Sai su ce wannan aure na mabanbanta addini ne don haka akwai haɗari. Sun ce mana kar mu kuskura mu yi," a cewarsa".

Lokaci na ƙurewa. Don haka ma'auranta sun yanke shawarar tserewa." Ina son kasancewa da Ayesha. Ba mu da zaɓi,"a cewar Santosh.

A ranar 22 ga watan Janairu, sun zo Delhi da nufin ganin burinsu ya cika na aure.

A cewarsu jirgin da suka shiga zuwa Delhi ne ya ba su damar kwashe tsawon sa'o'i tare a karo na farko cikin shekaru 13 da suka kwashe na soyayya.

Lokacin da suka isa, sun isa ofishin Dhanak, kungiyar da ta ba su masauki mai tsaro. Sun sanar da iyayyensu da jami'an ƴan sanda cewa suna Delhi. Sun koma gidan aka yi masu tanadi a ranar 29 ga watan Janairu.

Dhanak na taimakawa wajen aurar da masoya masu mabanbanta addini. Shugaban kungiyar, Asif Iqbal, ya ce suna karbar wayoyin mutane da dama da ke son aure tun lokacin da aka fitar da wannan doka mai cece-kuce a jihar Uttar Pradesh.

"Santosh na kuka lokacin da ya kira," a cewar Mr Iqbal.

Ma'aurata da dama na rasa ayyukansu lokacin da suka shiga ɓuya. Santosh da Ayesha na neman aiki. Sun shaida cewa suna cikin damuwa da tsoro amma sun ce yardar da suka yi da juna ke kara musu ƙwarin-gwiwar kasancewa tare.

"Soyayya na bukatar sadaukarwa," a cewar Ayesha.

Sun ce a halin yanzu, sun samu wajen zama kuma suna tare da juna.

"Sun ce soyayya ana cewa makauniya ce amma zan ce gaskiya ƙiyayyar da ake nunawa ce makauniya," a cewar Santosh.

Source: BBC