Kimanin magoya bayan Manchester United 200 ne suka shiga tsakiyar filin Old Trafford, inda suka yi zanga-zanga kan kin iyalan Glazer masu kungiyar.
Wannan lamarin ya faru ne tun kafin wasan Premier League da United za ta karbi bakuncin Liverpool ranar Lahadi a Old Trafford.
Sai dai daga baya an bukaci magoya bayan da kowa ya fice daga filin wasa, inda aka samu nasarar yin hakan.
Haka kuma an gudanar da zanga-zangar a wajen Otal din da 'yan wasa da jami'an United ke zaune kafin karawar ta Premier League.
Zanga-zangar ta samo asali ne, bayan da kungiyar ta kasance cikin shiga daga 'yan Premier da suka amince su kafa sabuwar gasar European Super League a watan jiya.
Tsarin bai samu karbuwa ba, wanda ya sha suka tun daga Fifa da Uefa da gwamnatin Burtaniya da masu ruwa da tsaki da dai sauransu.
Daga baya ne kungiyoyin Premier suka fice daga shirin, bayan matsin lamba, yayin da Atletico da Inter da Milan suka ce suma sun fita daga tsarin.
Daga karshe kungiya uku aka bari da suka hada da Real Madrid da Barcelona da kuma Juventus.
Magoya bayan United sun zagaye motar alkalin wasa Michael Oliver da kuma tsohon dan wasan kungiyar, Gary Neville a lokacin da za su shiga stadiya.
Babu wani tashin hankali ko lalata dukiya, an kuma bar Oliver da Neville sun shiga Old Trafford ba tare da tashin hankali ba a yayin zanga-zangar kin iyalan Glazer din.