A zahiri, abin da muka sani game da wannan janar din na soja, wanda bai kai shekara 40 ba, ba shi da yawa.
An haifi Janar Mahamat Idriss Déby a 1983 inda ya zama ɗaya daga cikin 'ya'yan marigayi Idriss Deby. Ana masa laƙabi da Mahamat Kaka, saboda a hannun kakarsa ya taso. Kaka na nufin kaka a larabcin Chadi.
A lokacin da mahaifinsa ya mutu, shi ne shugaban dakarun da ke tsaron shugaban kasa, kamar yadda wakilin BBC a Chadi ya bayyana. Wanda ya kara da cewa ya taka rawa a fafatawa da dama da sojoji suka ringa yi a tsawon rayuwarsa ta aiki.
A 2009, Mahamat Idriss Deby ya halarci yakin da Am Dam, wanda aka fafata da wani dan uwansa Timan Erdimi, da ke zama ɗan ɗan uwan tsohon shugaban ƙasar, a gabashin Chadi.
To amma duk da haka, dole ne a bayyana cewa ba fitacce ba ne a lokacin da mahaifinsa ke shugaban ƙasa. Sai dai ya ringa kula da samar da tsaro ga shugaban ƙasa, kuma yana da matukar fada a ji wajen kula da kayan yaƙi na sojojin ƙasar.
Duk da cewa ba shi da wata ƙwarewa wajen tafi da gwamanti, a yanzu Mahamat Deby Itno shi ne zai jagoranci gwamantin riƙon ƙwarya har tsawom wata 18.
A cewa mai magana da yawun rundunar sojan ƙasar, Colonel Azem Bermandoa Agouna, babban aikin majalisar rikon kwaryar da Mahamat yake jagoranta shi ne kare martabar ƙasar da tabbatar da tsaro a cikin gida "a wannan lokaci da ake yaki da 'yan ta'adda kuma dakarun shedan".
Kawu yanzu ba a sani ba ko sabon shugaban gwamnatin ta soja na da wani buri na siyasa.