Manchester City ta sanar da yin hasarar fam miliyan 126 a 2019/20 a kakar da aka ci karo da kalubalen cutar korona.
Kungiyar ta ce kimanin kaso 11 cikin 100 na kudin shiga fam miliyan 478 ta rasa, amma kididdigar bai hada da kudin da ta sayar da Leroy Sane zuwa Bayern Munich ba.
Sai dai kuma City na sa ran cin riba a kasuwancin da take gudanarwa a kakar bana.
An yi kiyashin hasarar fam miliyan 60 a shekara a kaka biyu da kungiyar za ta fuskanta tun farko.
An dakatar da gasar Premier League tsakanin Maris zuwa Yuni a shekarar 2020, sakamakon bullar cutar korona, kuma tun daga lokacin aka hana 'yan kallo shiga stadiya.
City wadda take ta daya a kan teburin Premier League na bana da tazarar maki 14 tsakaninta da Manchester United na fatan lashe kofi hudu a bana.
Kungiyar ta Etihad ta kai daf da na kusa da na karshe a Champions League da za ta fafata da Borussia Munchengladbach ranar Talata.
Za kuma ta buga wasan FA Cup da Chelsea ranar 17 ga watan Afirilu karawar daf da karshe, sannan za ta yi wasan karshe da Tottenham a Wembley a Caraboa Cup ranar 25 ga watan Afirilu.