Menu

Manyan kungiyoyin kwadago hudu da ke yajin aiki a Najeriya

 117877564 Mediaitem117877563 A cikin kungiyoyin kwadagon kungiyar likitoci masu neman kwarewa

Fri, 9 Apr 2021 Source: BBC

Manyan kungiyoyin kwadago hudu ne a halin yanzu suka tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani a Najeriya, lamarin da ya jefa 'yan kasar cikin mawuyacin hali.

Wadannan kungiyoyi sun hada da kungiyar likitoci masu neman kwarewa; kungiyar ma'aikatan kotu; kungiyar ma'aikatan kwalejojin fasaha da kuma kungiyar ma'aikatan majalisun dokokin jihohi.

Korafin da likitoci suka yi

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta tsunduma yajin aiki na sai abin da hali ya yi ne saboda abin da ta kira rashin isasshen albashi, da rashin biyan 'ya'yanta alawus-alawus da sauransu.

Shugaban kungiyar, Uyilawa Okhuaihesuyi, ya ce bukatun likitocin sun hada da neman biyansu kudaden da suke bin gwamnati bashi, da yin kwaskwarima kan dokar biyan alawus zuwa kashi 50 cikin 100, da kuma biyan inshora ga duk ma'aikacin lafiyar da ya mutu a bakin aiki na yaki da cutar korona.

Sai dai Ministan kwadago Chris Ngige, ya yi barazanar dakatar da albashin duk ma'aikacin lafiyar da ya shiga yajin aiki.

Bukatar cin gashin kai

Su kuma ma'aikatan shari'a na Najeriya karkashin kungiyar JUSUN sun tsunduma yajin aiki ne domin matsa wa gwamnati lamba kan a ba su 'yancin kansu.

Kungiyar ta soma yajin aiki ne ranar Talata 6 ga watan Afirilu, kuma a daukacin kasar.

Takardar da sakataren kungiyar I.M. Adetola ya rattaba wa hannu, ta bukaci mambobin kungiyar da ke jihohi da ofisoshinsu su mutunta matakin da aka dauka.

Wakilin BBC a Kano Khalifa Shehu Dokaji da ya zagaya wasu daga cikin kotunan jihar Kano, ya ruwaito cewa kotunan na rufe.

Wasu da aka kai domin yi musu shari'a an koma da su gidan gyaran hali na Kurmawa sakamakon yajin aiki da ma'aikatan shari'a suka fara.

Ya kara da cewa hatta kotun daukaka kara ta Musulunci da ke sakatariyar Audu Bako a jihar Kano, ita ma ta kasance a rufe.

Ma'aikatan kotun na yajin aikin ne kan yadda har yanzu gwamnatocin jihohi suka ki ba su gashin kai duk da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu kan hakan.

A watan Maris da ya wuce ne kungiyar ta yi taro inda ta bai wa gwamnonin wa'adin makwanni uku su amince da bukatarsu, idan kuma wa'adin ya cika babu wani sauyi za su tsunduma yajin aiki.

Abin da ya fusata ma'aikatan kwalejojin fasaha

A nasu bangaren, ma'aikatan kwalejojin fasaha da ke Najeriya wato polytechnic sun tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani ne ranar Talata.

Kungiyar ta ASUP ta ce gwamnati ta gaza biya musu bukatunsu sannan tun watan Mayun 2020 wa'adin da suka sanya wa gwamnatin ya cika.

Sun tafi yajin aikin ne bayan ganawa da Ministan Ilimi na Najeriya Adamu Adamu, wanda bayan sauraren bukatu da korafinsu bai ba su takamaimai lokacin da za a warware matsalar ba.

Kungiyar tana neman gwamnatocin wasu jihohi su biya mambobinta albashi da kuma alawus-alwasu da suke bin ta.

Majalisun jihohi 'sun zama kango'

Kungiyar ma'aikatan majalisun dokokin jihohi ta soma nata yajin aikin na kasa baki daya ne ranar 23 ga watan Maris na 2021 lamarin da ya gurgunta ayyukan majalisun dokokin jihohi 36 da Abuja.

Ta ce ta shiga yajin aikin ne saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da dokar 2018 da ta ba su damar cin gashin kansu ta fannin kudi.

Shugaban kungiyar, Usman Mohammed, ya ce yajin aikin ya zama wajibi saboda biris din da gwamnati ta yi wajen bin dokar.

A cewarsa, kungiyarsu ta bi dukkan hanyoyin da suka wajaba wajen ganin an rika ba su kudinsu kai tsaye amma hakan bai yiwu ba, lamarin da ya tilasta musu daukar matakin karshe - wato tafiya yajin aiki.

Sharhi

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum na ganin yajin aikin da wadannan kungiyoyi suka shiga zai yi tasiri sosai a kan lamuran da suka jibanci kiwon lafiya da wanzar da adalci da zartar da doka da dai sauransu.

Misali, wasu kotunan jihar Kano da ke Najeriya sun ba da umarnin sakin wasu da aka wanke da laifuka amma yajin aikin ya sa ba za a iya sakinsu a lokacin ba.

Kazalika yajin aikin da likitoci masu samun kwarewar aiki suka daka ya shafi marasa lafiya abin da masu sharhi ke ganin zai ta'azzara cutukan da suke fama da su, ko ma ya kai ga mutuwa.

Masu lura da lamura na ganin ya kamata gwamnatoci da kungiyoyin kwadago su samo wata hanya ta shawo kan takaddamar da ke tsakaninsu ba tare da yawaita yajin aiki ba.

Source: BBC