Ryan Mason kocin rikon kwarya da Tottenham ta nada, zai ci gaba da gudanar da aikin har zuwa karshen kakar tamaula ta bana.
Kocin ya maye gurbin Jose Mourinho, wanda ta kora ranar Litinin, bayan wata 17 da ya ja ragamar kungiyar.
Mai shekara 29, tsohon dan kwallon Tottenham ne, wanda ya yi ritaya a 2018, bayan da ya yi rauni a kokon kansa, yana kuma aiki da matasan kungiyar ne.
Ya fara jan ragamar babbar kungiyar Tottenham ranar Litinin, bayan da Mourinho ya hada ya nasa ya nasa.
Mason zai fara jan ragamar Tottenham wasan Premier League da za ta fafata da Southampton.
Daga nan zai ja ragamar kungiyar wasan karshe a Caraboa Cup da za ta kara da Manchester City a Wembley ranar 25 ga watan Afirilu.
Tottenham ta sanar da nada Chris Powell da kuma Nigel Gibbs a matakin mataimaka na rikon kwarya har da Michel Vorm, mai horar da masu tsaron raga.
Ledley King zai ci gaba da aiki a matakin babban kocin kungiyar domin taimakawa Mason.