Menu

Masu sa dokar kulle kan korona 'yan kama-karya ne - Bolsonaro

 117656069 5697a3aa B0d7 44bd B5b1 A0422b1b0742 Shugaban Brazil, Jair Bolsonaro

Mon, 22 Mar 2021 Source: BBC

Shugaban Brazil, Jair Bolsonaro, ya bayyana gwamnonin jihohi da shugabannin biranen kasar da ke sanya dokoki da matakan kulle don yaki da annobar korona ta karo na biyu a matsayin 'yan kama-karya.

Bolsonaro ya ce gwamnatinsa ta yi duk abin da za ta iya a kan annobar ta korona, a don haka yanzu lokaci ne da za a sake bude harkokin kasuwanci da tattalin arziki.

Shugaban yana jawabi ne ga daruruwan magoya bayansa da suka taru a kofar fadar gwamnati a Brasilia domin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Ya ce, "ku san abu daya shi ne, cewa ina samun kwarin guiwata ne daga ni kaina da kuma ku. Saboda haka idan wani yana tunanin cewa wata rana za ta zo da za mu sallama 'yancinmu to fa ya yi kuskure......"

Tun farkon bayyanar annobar ta korona, shugaban na Brazil ya yi watsi da irin kalamai da rahotannin da gargadin da ake yi a kan illar cutar.

Shugaban ya jinkirta sayen allurar rigakafin cutar, har ma kuma a baya bayan nan ya yi kira ga jama'a da su daina damuwa da fargaba da koke a kan cutar ta korona.

Sai dai abin da ke ba wasu 'yan kasar ta Brazil mamaki da tayar musu da hankali, shi ne Shugaba Bolsonaro na yin kalaman nasa na baya bayan nan ne a lokacin da cutar ta fi tsanani a kasar.

Lokacin da asibitoci ke cika da marassa lafiya, kuma yawan masu kamuwa da cutar da kuma wadanda take hallakawa ke ci gaba da karuwa.

Sama da mutane dubu biyu da dari biyu ne aka yi kiyasi akalla na mutuwa a sakamakon kamuwa da cutar a Brazil din a duk rana

Source: BBC