Wata matashiyar Kano a arewacin Najeriya da ta ƙera wata manhajar da za ta dinga bayar da rahotanni kan fyaɗe ya ja hankalin ƴan Najeriya a kafofin sada zumuna musamman Twitter.
Saadat Aliyu ƴar asalin jihar Kano ta samar da sabuwar manhaja ce 'Helpio App' mai bayar da bayanai kan cin zarafin mata wacce ta ƙaddamar a rumbun manhaja na wayoyin android wato Play Store a 2020.
Saadat ita ce shugabar kamfanin Shamrock Innovation mai ƙirƙire-ƙirƙiren fasaha kuma mai fafutikar ci gaban mata a fannin ƙirƙira.
Yadda aka gabatar da matashiyar a kanun labaran wasu jaridun ƙasar a matsayin 'Kano Lady' wato budurwa ƴar Kano shi ya ja hankalin ƴan Najeriya a kafofin sada zumuna musamman a Twitter.
"Kano Lady" na cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a shafin na Twitter tun daga ranar Litinin zuwa Talata inda kusan mutum 15,000 suka yi tsokaci akai.
Duk da ba kasafai akan samu mata ba a fagen ƙirƙirar fasaha a Najeriya musamman arewacin ƙasar ba, amma wasu na ganin ta cancanci yabo kuma ya dace a kira ta da sunanta na yanka.
Yawanci dai kafafen yaɗa labarai kan alaƙanta mutum da sunan garinsa musamman wanda ba sananne ba.