Menu

Matsalar tsaro: Majalisa ta bukaci Buhari ya sanya dokar ta baci a Najeriya

Buhari Army Chief Leo Irabor.jfif Shugaba Muhammadu Buhari

Wed, 28 Apr 2021 Source: BBC

Majalisar dokokin Najeriya ta bukaci gwamnati ta ayyana dokar ta-baci a kan tsaro tare da kara yawan sojoji da ƴan sanda, sakamakon tabarbarewa tsaro a ƴan kwanakin nan a yankunan ƙasar.

An yi asarar rayukan jama`a a sassan ƙasar da dama, ga kuma fargabar da ake yi cewa mayakan boko-haram sun ƙwace iko a wasu yankunan jihar Neja, har sun kafa tutocinsu.

Shawarar majalisar wakilai ga shugaba Muhammadu Buhari na ayyana dokar-ta-baci a harkar tsaro ta ƙasar, ya biyo bayan da mayakan Boko Haram suka kwace wasu yankuna 42 a jihar Neja

Wannan na cikin ƙudurori 12 da ƴan majalisar suka zartar bayan awowi sama da uku suna tafka muhawara.

Yan majalisar dokoki sun nuna damuwa game da yadda tsaro ke kara tabarbarewa a ƙasar, musamman ma kisan da ƴan bindiga suke yi wa jama`a, ciki har da jami`an tsaro.

Bukatar majalisar ta ayyana dokar ta-baci a kan harkar tsaro na zuwa ne yayin da ita kuma majalisar dattawa ta yanke shawarar gayyatar hafsoshin tsaron domin su yi musu bayyani.

Gwamnatin Buhari dai ta amsa cewa tana fuskantar matsaloli na tsaro kamar yadda mataimakin shugaban ƙasar Farfesa Yemi Osinbajo ya faɗa a ranar litinin cikin wata sanarwa amma ya ce "za mu iya magance su."

Sai dai masana dai na ganin akwai gazawar shugabanci da suka jefa Najeriya cikin wannan yanayi. Ana ganin abubuwan da ke faru a Najeriya na tattare da hatsari ga makomar ƙasar mai bambanci jama'a da kabila da addini.

Yadda tsaron ya kasance cikin mako guda

Fararen hula da jami'an tsaro da dama aka kashe a Najeriya cikin mako ɗaya.

Ƴan bindiga masu fashin daji da Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare tare da satar mutane domin kuɗin fansa.

Ɗaliban da Jami'ar Greenfield guda biyar da ƴan bindiga suka na cikin dalibai da dama da ake sacewa a makarantun arewa maso yammacin Najeriya

A kwanan nan gwamnatin Neja ta ce Boko Haram ta ƙwace wasu yankunan jihar tare da kafa tuta.

Mayaƙan Boko Haram da na ISWAP sun tsaurara kai hare-hare inda suka suka fito suka yi ikirarin kai hari a garin Geidam jihar Yobe inda har yanzu ba a tantance yawan mutanen da aka kashe ba.

Ƴan bindiga kuma sun kashe jami'an tsaro a jihar Rivers a harin da ake zargin ƴan IPOB ne suka kai.

Jami'an tsaron kasar na ta kokarin shawo kan karuwar hare-haren 'yan bindiga da ƴan fashi masu satar mutane da kuma waɗanda ake zargin 'yan a ware.

Source: BBC