Masana a Najeriya na ganin akwai gazawar shugabanci kan yadda tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar.
Sun ce halin da ƙasar take ciki a yanzu abu ne mai matukar tayar da hankali saboda girman matsalar tsaro da ke ci gaba da ɗaukar sabbin salo.
Sannan girman matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta ya raba hankalin jami'an tsaron ƙasar domin za su rasa inda ya kamata su fuskanta saboda yadda kusan sassan kasar na fama da matsalolin tsaro.
Malam Kabiru Sa'idu Sufi na Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke jihar Kano, ya danganta matsalar da gazawar shugabanci a matakin jihohi da gwamnatin Tarayya.
"Gazawar ta shafi matakin jiha da gwamnatin tarayya amma an fi danganta gazawar ga gawamnatin tarayya tun da jami'an tsaro masu dauke da makamai suna karkashin kulawarta ne," in ji shi.
Gwamnatin Buhari ta amsa cewa tana fuskantar matsaloli na tsaro kamar yadda mataimakin shugaban ƙasar Farfesa Yemi Osinbajo ya faɗa a ranar litinin cikin wata sanarwa amma ya ce "za mu iya magance su."
"Matsayin shugabanci shi ne a zauna a yi tunani kan matsalolin," in ji mataimakin shugaban Najeriya lokacin da ya karbi bakuncin basaraken Nasarawa Yakanaje Uke, Alhaji Dr. Ahmed Abdullahi Hassan a fadar shugaban ƙasa.
Malam Sufi na ganin babu kyakkyawar danganta tsakanin shugabancin tarayya da matakin jihohi waɗanda ke da alhakin shugabancin tsaro a jihohinsu kan shawo kan matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta.
Group Kaftin Sadiq Garba Shehu mai ritaya ya ce an samu sauƙi na yawan hare-haren Boko haram bayan hawan gwamnatin APC daga 2015 zuwa ƙarshen 2017 amma daga 2018 zuwa 2020 abubuwa suka rincaɓe.
A cewar masanin na tsaro, Najeriya yanzu ta kai za a iya kai hari lokaci daya a wurare daban daban na ƙasar.
Ya ce an yi sakaci a Najeriya ta yadda aka bari matsalolin suka kara ta'azzara ba tare da daukar matakai ba.
"Gwmnatin ba ta san zurfin ruwa ba sai da ta shiga - an yi alƙawalin magance tsaro duk da kafin zuwan APC matsalar Boko Haram da ƴan Neja Delta ake fuskanta kawai."
"Amma yanzu sai ga matsaloli sun ƙaru na kashe-kashe da sace-sacen mutane da fashi da hare-haren Boko Haram da kuma matsalar ƴan a ware na IPOB," in ji shi.
Ya ƙara da cewa sojoji da yan sanda da ake yaƙar Boko Haram tun kafin hawan gwamnatin Buhari da su ne kuma ake yaƙar yan fashi a Zamfara da Katsina da Neja da sauran sassan Najeriya.
Masanin na ganin an bar yawan jama'a da faɗin kasa da ke ƙaruwa ba tare da ɗaukar matakai na tsaro ba kamar yadda ake samun karuwar jama'a da faɗin kasa.
Ina matsalar ta ke?
Masanan na ganin akwai matsaloli da dama daga ɓangaren shugabanci da suka jefa Najeriya cikin wannan yanayi.
Malam Kabiru Sufi ya ce duk da akan tattauna da juna tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi kamar ziyarar da gwamnan Borno ya kai wa Buhari a kwanan nan amma a cewar masanin, "ba a kai wa ga cin nasara saboda ba a duba matsalar ta mahanga guda ɗaya."
Ya ce akwai ƙorafi daga jami'an tsaron na rashin kayan aiki kuma yawansu bai kai ga yadda za su tunkari matsalolin ba.
Haka kuma a cewar masanin har yanzu salon da aka daɗe ana amfani da shi ba a sauya ba ba domin kawo ƙarshen matsalolin.
Group Kaftin Sadiq Garba Shehu mai ritaya ya ce tun 1999 da aka dawo mulkin dimokurariyya babu gwamnatin da ta yi yunkurin karin sojoji da yan sanda da kudin da ake kashewa a kan tsaro da kuma makamai.
"Kayan da ake sayo wa ba su isa domin matsalar da Najeriya ke fuskanta ta zarta kayan da ake sayo wa," in ji shi.
Gwamnati na sake 'tsara tsarin tsaro'
Gwamnatin Tarayya dai ta sha cewa tana samun nasara a yaƙi da Boko Haram da kuma iya ƙoƙarinta na magance ƙalubalen tsaro
A ranar Talata gwamnatin Buhari ta ce tana sake shirya tsarin tsaronta a wani mataki na shawo kan matsalolin tsaron.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya tabbatarwa da yan Najeriya cewa gwamnatinsu za ta shawo kan matsalolin tsaron da ake fuskanta a yanzu
Ya kara da cewa "Wannan babbar kasa ce, don haka aikin 'yan sanda yana da matukar wahala. Akwai buƙatar mu sake tsara tsarin tsaro, wanda kuma muke yi a yanzu," in ji shi.
Osinbajo ya bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilan da ya sa ake samun matsaloli na tsaro a sassan kasar shi ne saboda wasu suna ganin ba tafiya da su cikin gudanar da lamura a yankunansu.
Me ya kamata a yi ?
Ana ganin abubuwan da ke faru a Najeriya na tattare da hatsari ga makomar ƙasar mai bambanci jama'a da kabila da addini.
Masanan na ganin ya kamata gwamnatin Najeriya ta ayyana dokar ta ba-ci ga matsalar tsaron Najeriya. "Duk wani babban aiki mai cin kudi a dakatar da shi a kafa dokar ta-baci," in ji Group Kaftin Sadiq Garba Shehu mai ritaya
Masanin ya ce idan ba zaman lafiya ba abin da za a iya yi.
Ya ce dokar ta-baci za ta ba shugaban kasa damar neman kudi domin tunkarar matsalar tsaro.
Sannan masanin ya bukaci a ƙara yawan jami'an tsaro na ƴan sanda da sojoji sannan a saki kayan aiki tare da sa ido ga yadda za a kashe kudaden.
A nasa ra'ayin, Malam Kabiru Sufi na ganin akwai bukatar a sauya salon yaki da ta'addanci - "domin yanzu ya nuna akwai gazawa"
"Dole a kawo sabon salo saɓanin wanda ake amfani da shi saboda matsalar ta yi ƙamari domin akwai yankunan da aka mamaye."
Ya ƙara da cewa ya kamata a diba abin da ya haifar da bazuwar ayyukan ƴan bindiga a yankunan Najeriya.
"Akwai bukatar ko wane yanki a diba tsarin da za a bi a magance matsalolin tsaron da yake fuskanta - kowane da dalilinsa daban kuma masu aikata shi daban kuma manufofinsu daban da hanyoyin da suke bi, don haka ko wane yanki sai an yi masa nashi nazarin yadda za a shawo kan matsalarsa."
Fararen hula da jami'an tsaro da dama ne aka kashe a Najeriya cikin mako ɗaya.
Ƴan bindiga masu fashin daji da Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare tare da satar mutane domin kuɗin fansa.
Ɗaliban da Jami'ar Greenfield guda biyar da ƴan bindiga suka na cikin dalibai da dama da ake sacewa a makarantun arewa maso yammacin Najeriya
A kwanan nan gwamnatin Neja ta ce Boko Haram ta ƙwace wasu yankunan jihar tare da kafa tuta.
Mayaƙan Boko Haram da na ISWAP sun tsaurara kai hare-hare inda suka suka fito suka yi ikirarin kai hari a garin Geidam jihar Yobe inda har yanzu ba a tantance yawan mutanen da aka kashe ba.
Ƴan bindiga kuma sun kashe jami'an tsaro a jihar Rivers a harin da ake zargin ƴan IPOB ne suka kai.
Jami'an tsaron kasar na ta kokarin shawo kan karuwar hare-haren 'yan bindiga da ƴan fashi masu satar mutane da kuma waɗanda ake zargin 'yan a ware.