Dan jaridar da ke bayar da labarai kan kwallon kafa Guillem Balague ya ce Paris St-Germain ba ta da niyyar barin kocinta Mauricio Pochettino ya bar su.
Tottenham ta tuntubi kocin mai shekara 49 game da yiwuwar komawa can, inda ya kwashe shekara biyar yana aiki.
Kungioyar tana son sake daukar Pochettino ne bayan da aka samun ingantuwar dangantaka da mamallakin kungiyar Daniel Levy.
"Yana fatan komawa Ingila, amma tuni ya soma shirin kakar wasa mai zuwa da masu ruwa da tsaki na PSG," in ji Balague.
"PSG ba ta da niyyar barinsa ya tafi kuma ta yi mamaki kan yadda ake cewa za ta sallame shi domin kuwa babu kanshin gaskiya."
Balague ya ce annobar korona - da matsalolin da ta haddasa na hana tafiye-tafiye - ta sa rayuwa ta yi wa dan Argentina wahala a Paris, domin kuwa rabin iyalansa suna zaune a London.
Tottenham ta kori Jose Mourinho, kocin da ya maye gurbin Pochettino, a watan jiya kuma tana nazari kan yadda za ta samu wanda zai zama sabon koci.
Kocin makarantar horas da 'yan wasa Ryan Mason yana rikon kwarya zuwa karshen kakar wasan bana. A karkashin jagorancinsa, Spurs ta sha kashi a hannun Manchester City a wasan karshe na Carabao Cup kuma ta kare a mataki na bakwai a gasar Firimiya ta Ingila ta kakar.