Menu

Me ya sa wasu mutane suke jin dadi idan sun yi ashar?

 118231198 3f14f437 0e44 49e4 B187 0f113a3f5a4c Me ya sa idan mutum ya yi ashar sai ya ji ya gamsu?

Tue, 11 May 2021 Source: BBC

Me ya sa idan mutum ya yi ashar sai ya ji ya gamsu?

Ko dai don mun san ba dai-dai ba ne ko kuma dai wani abu ne ke sauyawa a ƙwaƙwalenmu da jikkunanmu idan muka yi ashar?

Duk mun taɓa tsintar kanmu a wani yanayi, misali mu dauje ɗan yatsanmu na ƙafa ko kuma mu tsinci kanmu a cunkoson motoci ko mun haɗo ɗan shayinmu ya ɓare. Kawai sai mu ji mun ƙundumo ashar.

Kuma muna yin hakan sai mu ji sauki a ranmu.

Lallai ne wasu sun fi wasu yin ashar, kuma wani lokaci ma wasu mutanen kan yi ashar a lokacin da suka tsinci kansu cikin farin ciki.

Amma dai ko wace al'ada da yare suna da salon ashar ɗinsu... kuma wataƙila ma ba mutane ne kawai ke yin ashar ba (za mu duba wannan nan gaba).

Don haka, me ke sa wa a yi ashar?

Mene ne ashar?

"Yin ashar abu ne mai wuyar sha'ani," a cewar Dokta Emma Byrne, wata ƙwararriya a harkar ashar kuma marubuciyar littafin Swearing Is Good For You.

Ta ce ashar yare ne da muke amfani da shi idan an shammace mu ko idan mun yi mamaki ko farin ciki ko idan mun ga abin ban dariya ko abin takaici... amma wani ɓangare ne na al'ada da wata al'umma ko ƙasa ko addini kawai ke fahimta.

"Mun amince da ashar, kuma amicewar ta ƙunshi cewa yinta abin ƙi ko kuma abin kunya ne a al'adance: Wasu al'ummomin na ganin ambato wasu ɓangarori na jiki abin kunya ne yayin da wasu kuma suke ganin sunayen wasu dabbobi da wasu cutuka da dai sauransu ne abin kunya," a cewar Dokta Byrne.

Amma akwai wani abu guda dangane da yin ashar. " Don ta iya sosa rai, sai idan ka ambato wani abun kunya a al'ummar."

To don haka me ya sa muke yin ashar?

"A lokacin da muke cikin yanayi na matsi, ko wani abu ya faru na ba-zata ba ma sanin lokacin da muke yin ashar. Kuma sai mu ɗan samu nutsuwa!" a cewar Gadi, wani mai sauraren BBC.

Kuma wasu masu saurarenma sun yarda da hakan:

"Lokutan da nake ashar kan zama lokutan farin ciki ko mamaki ko tsannain da-na-sani, ko jin raɗaɗi ko fushi. Da alama ashar wata hanya ce ta bayyana yadda kake ji a ranka," a cewar Mikhail.

"Sai dai kawai ka ji ya fita daga bakina ba tare da na yi tunani ba kuma sai in ji sanyi a raina," a cewar Chimes E.

"Ban fiye yin ashar ba. Ina ganin idan ka fiye yi, sai ka daina jin nauyinta a bakinka. Gara ka riƙa yi jifa-jifa idan buƙatar yinta ta taso," a cewar Clara.

Babu shakka akwai mutanen da kwata-kwata ba sa yin ashar, amma da yawanmu za su fahimci abin da masu saurarenmu suka ambato- irin gamsuwar da ake samu bayan yin ashar.

Dakta Byrne ta bayyana cewa daya daga cikin abubuwa masu ban sha'awa da ta taba cin karo da su a lokacin binciken nata ( da suka shafi kiwon lafiya) su ne cewa ko da za su iya rasa damar yin magana, amma ba gabaki daya ba.

"Idan ka cire bangaren dama na wani mutum, ko kuma wani wanda bangaren damarshi ya samu nakasu, sukan rasa akasarin harsunsansu, abin da za ka iya ganowa kawai shi ne duk da haka za su iya yin ashar ,'' in ji Dokta Byrne.

"Da alamu mukan danganta babbar damuwarmu ne da wasu nau'ukan harsuna, kuma suna ajiye a wurare daban-daban ne daga sauran harsunan.

Za ka iya cire (bangaren kwakwalwar) kana ka kassara daukacin damar da wani ke da ita ta amfani da harsunan ta yadda zai kasance kamar da gangan ne kuma a tsare kamar yadda nake yi a halin yanzu. Amma kuma, za su iya ci gaba da yin ashar din.

"Ana danganta ashar kai tsaye da shiga damuwa, cewa wasu jijiyoyi kan bukaci motsawa don furta wasu kalamai da ke ajiye a wurare da dama. Don haka muna da ma'ajiya ta shirin ko-ta-kwana don lokacin da za mu iya bukata,'' in ji Dokkta Byrne.

Ko wata kalmar ta daban na iya maye gurbin ashar?

"Ina tunanin ko akwai wani yanayi na yin ashar a lokacin da kake jin zafi ko bacin rai, kuma ko shin zai iya taimakawa," in ji dakta Richard Stevens, wani babban malami kuma kwararre a fannin halayyar dan adam da ke Jami'ar Keele, kana mutumin da ke lura da ''dakin binciken yin ashar'' inda suke gudanar da binciken.

Daya binciken na duba ko ashar kan taimaka wajen saukaka ciwo ko damuwa, ko kuma matsanancin hali, da ya hada da saka hannayenka cikin bokiti mai cike da kankara, don ganin yanayin tsawon lokacin da za ka iya jurewa.

Ya gudanar da wannan gwaji ne a kan mutum guda, sau biyu: daya ta hanyar amfani da kalamai na ashar, kana daya ta hanyar amfani da kalamai masu mutuntaka.

Kwararrun sun gano cewa lokacin amfani da ainihin kalaman ashar, mutane kan iya jurewa sosai kana sukan iya jure dadewar hannayensu a cikin kankarar, amma kuma akwai wata matsala a lokacin da ake amfani da kalaman da ke maye gurbinsu: ba su yi amfani ba saboda ba su da wani tasiri a kan ainihin kalaman ashar din.

Amma me ya sa haka?

"Galibi mukan ga karuwa a yanayin bugawar zuciya a lokacin halin yin ashar. idan aka kwatanta da na kalmar da ba ta ashar din ba.

Da alamu hakan na nuni da yanayin shiga damuwar da kan sa a yi ashar din, kuma mun san cewa ashar wani irin harshe ne na shiga halin damuwa,'' in ji dakta Stevens.

Dakta Stevens ya kara da cewa: "Don haka binciken aikin namu ya nuna cewa a lokacin da mutane ke yin ashar a ciki halin bacin rai ko jin zafi, sukan rage kaifin damuwar tasu, kuma yakan zama wani maganin rage radadin damuwar (a lokacin da kake cikin tsananin jin zafin ko damuwa), wanda wani bangare ne na yakar duk wani yanayin damuwa,"

"Ban cika yin ashar ba,'' in ji Colin, daya mai sauraron: ''Amma shekaru kadan da suka wuce, sai da aka ceto ni daga kan wani tsauni bayan wani hadari.

"Na samu muguwar karaya a kafadata kuma sai da aka saka ni a kan wani allo wurin sauko da ni daga kan tsaunin. Kowa ce gargada wani tsananin ciwo ne. Kuma abin da na iya yi shi ne surutai da ba su da kan gado yayin da ake sauko da ni daga tsaunin. Babu wasu kalamai da zan iya yi a lokacin."

Ashar daga cikin harsuna

Sanin iya abin da muka sani, shin ashar duk daya yake a cikin kowace al'ada?

Da alamu BBC ta samu wasu masu sauraro wadanda ke iya furta kalamai marassa dadi, da a shirye suke su taimaka mana har ila yau:

"Sifaniyanci, harshe ne mai cike da dabaru wajen yin ashar,'' in ji Clara, "saboda a lokacin da ka ji wani ya shiga mummunan bacin rai, za ka samu cikakkun bayanai, da kuma cikakkun labarai da irin na sau labarin. Duka a cikin ashar.''

Daga Malta, Jane ta ce: "Abu marar dadin ji da mai yiwuwa za ka iya fada wa mutum shi ne ya fassara 'maniyyi'. Wanda wani abu ne na ba kasafai ba saboda a wasu harsunan ba za ka iya kiran wani ka fada masa haka ba, ba tare da an yi maka wani mugun kallo ba.''

"Rashanci harshe ne mafi kyau wajen yin ashar. Akwai abubuwan bata rai da dama, kusan komai zai iya kasancewa mai bata rai!

Al'adar yin ashar a nan ta samu wurin zama sosai a adabinmu. Kuma zai yi wuya a samu ɗan Rasha da ba ya ashar," a cewar Mukhail.

"Akwai wasu kalaman ashar a yaren China, wanda ke nufin saba wa kakanninka tun daga na 18,: a cewar Jacqueline, "kamar 'zan yi wa mahaifiyarka abu kaza, zuwa kakarka zuwa dukkanin kakanninka har zuwa na 18'.

Akwai wata kalmar ashar a China da ta ƙunshi ƙwayayen kunkuru, kuma wadda ta samo asali daga camfin da ke cewa uwar kunkuru na da yawon banza... don haka idan aka kira mutum ƙwan kunkuru ana nufin ba a san waye mahaifinsa ba.

Don haka, duk da cewa ashar ya sha bambam a faɗin duniya, abu ne da a ko ina a faɗin duniyar ana yin sa.

Shin ya batun dabbobi, suna yin ashar?

Sai dai ba ɗan Adam ne kawai ke yin ashar ba. Dokta Emma Byrne ta ce akwai bincike mai ɗaukar hankali da aka gudanar kan birrai da ya ƙunshi riƙon birran kana a kai su cikin wani iyali na birrai masu yawa.

Wasu ƙwararru a harkar birrai a Amurka Deborah and Roger Foots "sun yi magana ne a gaban birran ta hanyar amfani da maganar kurame. Kuma sun koya wa birran yadda ake kwatanta abubuwa da dama, a cewar Dokta Byrne.

A dawa, birrai na magana ne ta hanyar yin wurgi da kashi - amma Deborah da Roger Foots sun tabbatar sun hana su yin haka kuma sun koya masu amfani da makewayi.

"Suna iya yin haka, sai birran suka fara amfani da maganar kuramen da suka koya da ke bayyana 'jin kashi ko ƙazanta' yadda masu amfani da Turancin Ingilishi ke amfani da kalmar da ke bayyana jin kashi, a cewar Dokta Byrne.

"Birran na amfani da maganar kuramen su bayyana takaicinsu, suna amfani da ita wajen nuna fushi, sai suka fara amfani da maganar suna kiran sauran birran 'ƙazamin biri’ wanda ita ce kamar ashar mafi muni da za su iya yi."

Ba a nan abin ya tsaya ba, "birran nan na barkwanci da kalmar kashi a maganar kurame," a cewar ƙwararriyar.

"Roger da Deborah Foots sun yi rubutu kan tafiya a ɗakin gwaji suna sauraren birran suna buga bayan hannunsu a ƙasan haɓarsu (alamun datti) da ƙarfi har sai haƙoransu na sama da na ƙasa sun bugi juna, a cewar Dokta Byrne.

Don haka, maimakon jefa wa juna kashi, birran nan sun koyi amfani da maganar kurame su zagi juna.

"Kuma a ganina wannan shi ne ɓangaren binciken da ya fi ɗaukar hankali: Fahimtar cewa da zarar an nuna rashin dacewar abu ko kasancewarsa abin kunya, ana iya samar da ashar daga cikinsa," a cewar Dokta Byrne.

Eva Ontiveros ce ta tace kuma ta gyara.

Source: BBC