Mohamed Bazoum ya nada sabbin ministoci a Jamhuriyar Nijar
Sabon shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum
Fri, 9 Apr 2021
Source: BBC
Shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya nada sabbin ministoci da za su yi aiki a gwamnatinsa.
Sanarwar da Sakataren Gwamnatin kasar ya fitar ranar Laraba ta ce an nada sabbin ministoci 33, shida daga cikinsu mata ne.
Hakan na nufin adadin ministocin ya ragu idan aka kwatanta da ministoci 43 da suka yi aiki a gwamnatin tsohon shugaba Mahaman Issoufou.
An nada ministocin ne a yayin da sabon firaiministan Jamhuriyar ta Nijar Ouhoumoudou Mahamadu ya sha rantsuwar kama aiki.
Ga jerin ministocin:
Ministan harkokin waje - Hassoumi Masaoudou
Ministan kasa a fadar shugaban kasa - Rhissa Ag Boula
Ministan tsaro - Alkassoum Indattou
Ministan cikin gida - Alkache Alhada
Ministan koyon ayyukan hannu - Kassoum Mahaman Moktar
Ministan illimi mai zurfi - PHD Mamoudou Djibo
Ministan kiyon lafiya - Dr Illiassou Idi Mainasara
Ministan ma'adanai - Mme Ousseini Hadizatou Yacouba
Ministan sadarwa ta hanyoyin zamani -Hassane Baraze Moussa
Ministan Sufuri - Oumarou Mallam Alma
Ministan agajin gaggawa - Lawan Magaji
Ministan kiyo kakakin gwamnati - Tijani Abdukadri
Ministan gine-gine - Hamadou Adamou Souley
Ministan Shari'a - Dr Biubacar Hassan
Ministan yada labaru da hulda da sauran hukumomi - Zada Mahamado
Ministan Kudi - Ahmat Jidoud
Ministan kasuwanci da masana'antu - Gado Sabo Moktar
Ministan ayyukan noma - Dr Alambedji Abba Issa
Ministan zane-zane da gidaje da tsaftar muhali - Maizoumbou Laoual Amadou
li> Ministan fasali - Abdou Rabiou
Ministan man fetur da makamashi - Mahamane Sani Mahamadou.
Ministan kula da al'adu, yawon bude ido da ayyukan hannu -Mohamed Hamid
Ministan inganta kasa da cigaban ci gaban karkara - Maman Ibrahim Mahaman
Ministan kula da yaya mata da kari'a kananan yara - Mme Allahoury Aminata Zourkaleini
Ministan illimin kananan makarantu - Dr Rabiou Ousman
Ministan Albarkatun ruwa - Adamou Mahaman
Ministan kwadago - Mme Ataka Zaharatou Aboubacar
Ministar muhalli da yaki da kwararar hamada - Mme Garama Saratou Rabiou
Ministar kula da ayuka da kariyar al'umma - Dr Ibrahim Boukary
Ministan matasa da wasannin motsa jiki - Sekou Doro Adamou
Karamin minista a ma'aikatar kudi - Mme Gourouza Magaji Salmou
Karamin minista a ma'aikatar cikin gida - Dardaou Zaneidou
Karamin minista a ma'aikata harkokin waje - Youssouf Mohamed Almoktar