Menu

NNPC: Kamfanin mai na Najeriya ba zai saka kudi a asusun gwamnati ba a watanni masu zuwa

Nnpc Tower Nigeria NNPC ne kamfanin mai na Najeriya

Sat, 1 May 2021 Source: BBC

Rahotanni sun ce kamfanin man Najeriya NNPC ya ce ya ce ba zai iya sanya ko sisin kwabo ba a asusun tarayya a watan Mayu mai zuwa.

Kamfanin ya ce hakan ya zama wajibi ne saboda gibin da ya samu a kudaden shiga Naira biliyan dari daya da goma sha daya (N111bn) a watan Fabrairun da ya gabata.

Ya kuma ce ga yawan kudaden da yake kashewa wajen bayar da tallafi ko rangwamen farashin man fetur a kasar wato subsidy.

Wata majiya a kamfanin na NNPC ta tabbatar wa da BBC cewa lallai kamfanin ya rubuta wasika ga kamfanin babban akanta na Najeriya yana shaida masa halin da ake ciki.

Majiyar ta kuma ce a duk wata, kamfanin kan kashe Naira biliyan dari daya wajen biyan kudaden tallafin mai da nufin saukaka farashin albarkatun man fetur da jama'ar kasar ke amfani da su.

NNPC din dai na nuni da cewa wannan yanayi ya sanya shi cikin tsaka mai wuya, da idan ya cigaba da bayar da gudumawa ga asusun tarayya, ba zai iya biyan tallafin mai ba, lamarin da ka iya sa farashin man ya yi tashin gwauron zabi a kasar da kuma kara tsadar rayuwa ga talakawan kasar.

A bangare guda kuma idan ya biya tallafin b azai iya saka kudi ga asusun tarayya ba kuma shine matakin da ya dauka a yanzu.

Sai dai kuma wannan shi ma rashin bayar da gudumawa da baitulamlin zai iya yin illa ga kudaden shuga na gwamnatoci a matakan tarayya, da jihohi, da kuma kananan hukumomi, abinda wasu ke ganin ka iya shafar gudanar da ayyuka da kuma biyan albashin ma'aikata.

Najeriya na daga cikin kasashen da ke kan gaba a duniya wajen arzikin mai, kuma kasa ce da arzikin ta ya dogara kacokan kan kudaden shiga daga man fetur.

Kan haka ne tattalin arzikin ya gigita a sakamakon mummunan faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya wanda annobar korona ta haddasa.

A bangare guda kuma, kasar ba ta da managartan matatun man fetur, wanda ya tilasta mata sayar da danyen man ta a kasashen waje, kana ta sayo tatattun albarkantun man domin amfanin jama'a a cikin kasar.

A wannan tsari mai rauni ne kuma kasar ke biyan kudaden tallafin mai domin saukaka farashin man a gidajen mai a kasar.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum suns ha kokawa cewa wannan tsarin na cike da almundahana ta yadda 'yan kasar ke cewa sun kasa fahimtar yadda ake tafiyar da tsarin.

Source: BBC