Menu

NYSC: Matasa na muhawara kan soke tsarin hidimar ƙasa

 118658216 Youthcorpmemb A soke shirin hidimar kasa saboda matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya, inji dan majalisa

Tue, 25 May 2021 Source: BBC

Ƙudirin doka da zai hana yin hidimar ƙasa a Najeriya ya wuce mataki na biyu a zauren Majalisar Wakilan Najeriya.

Honarabul Awaji-Inombek Abiante mai wakiltar yankin Opobo/Nkoro ne ya miƙa ƙudirin da ke da burin soke shirin na NYSC, kamar yadda ya ce saboda matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya.

Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce a shafin sada zumunta na Twitter a ƙasar musamman a tsakanin matasa inda wasu ke ganin soke shirin mataki ne mai kyau yayin da wasu kuma ke ganin bai dace a soke ba.

Hidimar ƙasa ta NYSC na buƙatar duk ɗan Najeriyar da ya kammala makarantar gaba da sakandire da shekarunsa ba su haura 30 ba ya yi wa ƙasar hidima ayankin ƙasar da ba nan ya fito ba.

Misali, ƴan kudu a kan tura su arewacin ƙasar su ma ƴan arewa a kan tura su kudancin ƙasar.

Amma kafin nan sai an yi masu atisaye mai kama da na sojoji kafin tura su gudanar da ayyuka a makarantu ko asibitoci ko bankuna da dai sauran hukumomi.

Sai dai kawo yanzu, matsalar tsaro na nema ta zama barazana ga wannan tsarin musaman yadda sace-sacen mutane ya yi ƙamari a Najeriyar.

Source: BBC