Wasan kwaikwayo mai suna Nomadland ya yi nasara a rukuni uku na gasatt Oscars ciki har da matsayi na daya a fannin fitattun hotuna , yayin da fitattun taurarin fina-finan Birtaniya Sir Anthony Hopkins da Daniel Kaluuya suna lashe kyautar gwarazan taurari.
Daraktar Nomadland Chloe Zhao ta kafa tarihin zama mace ta farko da ba baturiya ba da ta lashe kyautar gwarzuar mai bayar da umarni.
Sir Anthony, mai shekara 83, shi ne mutumin da ya fi yawan shekaru da ya lashe gasar gwarzon tauraro, yayin da Kaluuya ya kasance dan wasan kwaikwayon Birtaniya bakar fata na farko da ya yi nasara a gasar Oscar - a bangaren taimaka wa babban tauraro.
'Yar fim din Birtaniya wadda ta zama mai rubuta labari da bayar da umarni Emerald Fennell ta zo ta daya a fannin rubuta wasan kwaikwayo.
Ta yi nasara a kan rubuta kirkirarren wasan kwaikwayo da fim din Promising Young Woman, wanda kuma ita ce ta bayar da umarni.
Frances McDormand ta lashe kyautar gwarzuwar tauraruwa saboda rawar da ta taka a fim din Nomadland, yayin da fitacciyar tauraruwar fina-finan Koriya ta Kudu Yuh-Jung Youn ta lashe kyautar gwarzuwa a fannin mai taimaka wa taurari a fim din Minari.
An bayar da kyautukan ne a a dakin taro na TUnion Station da ke birnin Los Angeles na Amurka, yayin da a bangagare daya aka bai wa taurari mazauna nasu kyautukan a wani dakin taro da ke birnin London - kodayake Sir Anthony bai halarci kowanne daga cikin bukukuwan ba
Sir Anthony ya doke Boseman
Sir Anthony ya lashe kyautar gwarzon tauraro saboda rawar da ya taka a matsayin mai fama da cutar mantuwa a fim din The Father, shekara 29 bayan ya lashe kyautar Oscar ta farko a fim din The Silence of the Lambs.
Nasarar d ya yi ta yi matukar bayar da mamaki. An sa ran marigayi Chadwick Boseman, wanda ya mutu yana da shekaru 43 a watan Agustan da ya gabata ne zai lashe kyautar saboda rawar da ya taka a fim Black Bottom na Ma Rainey.