Menu

PSG ta fi kokari a Champions League fiye da a Ligue 1

 117887434 Psg Yan wasan kungiyar PSG

Fri, 9 Apr 2021 Source: BBC

Bayan da Paris St Germain ta dunga cin karo da koma baya a gasar Champions League a shekarun baya, yanzu ta dauki hanyar jan ragamar gasar Zakarun Turai.

Kungiyar ta Faransa ta kai wasan karshe a bara, inda Bayern Munich ta doke ta 1-0 ta kuma lashe kofin, sai dai tun daga fara wasannin bara, PSG ta yi rashin nasara a karawa hudu daga 20 da ta yi.

Amma idan ka kwatanta kokarin kungiyar a Ligue 1 a bana an doke ta a fafatawa takwas, tana kuma ta biyu a kan teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Lille ta daya.

Cikin watan Janairu PSG ta sallami Thomas Tuchel ta kuma nada Mauricio Pochettino domin daga martabar kungiyar a gasar ta Champions League da ba ta taba dauka ba.

PSG ta yi nasarar doke Barcelona da Manchester United da Real Madrid a kaka biyu ta zakarun Turai da ta wuce da hakan ke kara nuna karfin da kungiyar ke kara yi.

A wasannin bana kungiyar ta Faransa ta je ta doke Barcelona har gida ta kuma fitar da kungiyar a gasar Champions League.

Ranar Laraba PSG ta je har Jamus ta ci Bayern Munich 3-2 mai rike da kofin wadda ta yi wasa 19 a gasar zakarun Turai ba a doke ta ba.

Rabon da Bayern ta yi rashin nasara a Champions League tun ranar 13 ga watan Maris din 2019, inda Liverpool ta doke ta da ci 3-1.

Ranar 13 ga watan Afirilu PSG za ta karbi bakuncin kungiyar Jamus a wasa na biyu a quarter finals, kuma a ranar za a auna kokarin kungiyar Faransa ko za ta kai karawar gaba.

Source: BBC