Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraron Dr Bashir Aliyu Umar
A daren Lailatul Qadri da ke goman karshe na watan azumin Ramadan ne Allah ubangiji ya saukar da Alkur'ani mai girma, abin da ya sa Musulmi suke neman dacewa da wannan daren.
Duk da cewa babu tabbacin wani dare da aka ware da cewa shi ne daren na Lailatul Kadri, amma hadisai da malamai sun nuna cewa daren yana wakana ne a mara ta karshen kwana goma na watan Ramadan.
Dararen mara dai kan fara tun daga daren 21 da daren 23 da 25 da 27 da kuma 29.
Hakan ne ma ya sa wasu Musulmin yin tsumbure dangane da ibadun da ake son yi wato idan sun yi wannan dare sai su huta a wani daren inda za su sake kaimi a daren mara na gaba.
To sai dai malamai sun ce ba a yi wa ubangiji wayo, inda suke shawartar masu neman dacewa da su raya dukkanin daren goman karshen azumin Ramadan.
Dr Bashir Aliyu Umar, limamin masallacin Alfurqan da ke birnin Kano, ya lissafa wasu abubuwa guda 10 da ya ce su ne jagoran mai neman dacewa da daren Lailatul Kadri, kamar haka:
Niyyar neman yardar Ubangiji
Neman gafara ga Ubangiji kasancewar samun rabauta ya ta'allaka ne ga irin afuwar da Allah ya yi wa dan adam a wannan dare.
Wankan tsarki tsakanin Magriba da Isha'i ko kuma bayan Isha'i kamar yadda ya zo a sunnar Annabi Muhammad (SAW). Har wa yau, yana da kyau a sanya tufafi mai kyau domin daren tamkar Idi ne.
Tashin iyali domin neman rabauta kamar yadda ya zo a sunnah cewa Annabi SAW duk dare yana tashin iyalansa domin yin ibada.
Raya kowanne dare da sallah da sauran ibadu daidai gwargwado ba tare da yin barcin da ya wuce kima ba. Saboda ana son mutum ya kaurace wa makwancinsa a wadannan darare.
Mutum ya guji rigima ko musu ko da kuwa da iyalinsa ne domin musu da jayayya na janyo daukewar rahama.
Yawan yin addu'ar da Annabi ya koya wa matarsa, Aisha wato Allahumma Innaka Afuwun Tuhibbul Afwa Faafu anna.
Mutum ya kyautata wa mahaifansa a dukkan dararen goman karshe, abin da zai sa su yi farin ciki da mutum.
A kuma yawaita addu'ar neman 'yantawa daga wutar jahannama.
Sannan a yi tawassuli da dararen goma wajen neman Allah ya fitar da Musulmi daga sharrin annobar korona.