Ranar Asabar, Real Madrid ta doke Elche da ci 2-1 a gasar La Liga karawar mako na 27 da suka fafata a Stefano Di Alfredo.
Dani Calvo ne ya fara ci wa Elche kwallo a minti na 61 daga baya Real ta farke ta hannun Karim Benzema ya farke, sannan ya kara na biyu daf da za a tashi.
Kyaftin din Real, Sergio Ramos ya buga karawar ya kuma zama na biyu a tarihin gasar da aka ci wasanni da yawa a gasar da shi a cikin fili.
Ramos ya buga La Liga sau 508, har da wasanni 39 da ya yi a Sevilla ya kuma ci kwallo 74 kawo yanzu.
Kawo yanzu an ci wasa 334 da shi a gasar, ciki har da 315 a Real Madrid da 19 a Seville, kuma ya yi kan-kan-kan da Casillas a yawan buga wasannin da aka yi nasara.
Lionel Messi na Barcelona ke kan gaba a tarihi da lashe karawa 377 a gasar ta Spaniya.
Ramos ya lashe kofin La Liga biyar a shekarar 2006/07 da 2007/08 da 2011/12 da 2016/17 da kuma 2019/20.
Real tana ta biyu da maki 57 a teburin La Liga, yayin da Barcelona wadda za ta buga ke mataki na uku da maki 56.