Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya ce kusan yara miliyan 26.5 ba sa samun isasshen ruwan bukatun yau da kullum a Najeriya.
Wakilin UNICEF a kasar, Peter Hawkins ne ya bayyana haka a Ranar Ruwa Ta Duniya.
Mai Magana da yawun Hawkins Ijeoma Onuoha-Ogwe ce ta sanar da hakan a sanarwar da ta fitar, tare da karawa da cewa kashi 29 cikin 100 na yaran kasar suna fama da karancin ruwan mu'amalar yau da kullum.
Sanarwar ta ci gaba da cewa Najeriya na cikin kasashe 37 da kananan yara ke fuskantar matsalar rashin ruwa.
Yayin da ake bikin Ranar Ruwa Ta Duniya, sama da mutum biliyan 1.42 ciki har da yara miliyan 450 na rayuwa ba tare da isasshen ruwa ba, kamar yadda sabon binciken da UNICEF ta gudanar ya bayyana.
Hakan na nufin yaro 1 cikin 5 a fadin duniya ba ya samun tsaftataccen ruwan bukatun yau da kullum.
Rahoton na UNICEF ya nuna matukar damuwa kan halin da yara ke ciki a Najeriya, saboda yawan wadanda abin ya shafa.
Rashin ruwan ya shafi wasu yankunan da baki daya ba a samun ruwan, yayin da wasu yankunan kuma ruwan ba shi da tsafta.
Yawancin mazauna yankunan sun dogara ne da ruwan da ake saye, ko inda a kan shafe mintina 30 ko sama da haka kafina a debo ruwan.
Arewaci da Kudancin Afirka na daga cikin wuraren da suka fi yawan yaran da suke fama da rashin ruwan inda kashi 58 cikin 100 na mazauna yankunan ba sa samun ruwan amfani a kowace rana, in ji UNICEF.
Sai kuma Yammaci da Gabashin Afirka, inda kashi 31 cikin 100 na yara ke cikin wannan matsala ta rashin ruwa.
Bincike ya gano cewa yankunan da suke dogaro ga ruwan rijiya na cikin gagarumar matsala, musamman ƙananan yara da kan kasa zuwa makaranta sakamakon kafewar rijiyoyin da sai sun yi doguwar tafiya kafin samun ruwa.
Yayin da fari ya fada wa irin wadannan yankunan, lamarin na shafar cimakar da ake sarrafa wa yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki.
UNICEF ya kara da cewa ba nan matsalar yaran ke tsayawa ba, hatta lokutan ambaliyar ruwa sukan yi fama da rashin lafiyar da ruwa maras tsafta ke haddasawa.
Wakilin na UNICEF ya ce yayin da ake fama da rashin ruwa a Najeriya, kananan yara ba sa samun isasshen ruwan wanke hannu domin kauce wa kamuwa da cututtuka.
"Kididdigar da muka fitar ta nuna yara a sama da kasashe 80, na rayuwa a wuraren da ba a samun ruwa, kuma suna bukatar tsananin taimako wanda ana bukatar daukar matakin gaggawa domin shawo kan matsalar.
Wadannan kasashe sun hada da Afghanistan da Burkina Faso da Habasha da Haiti da Kenya da Najeriya da Nijar da Sudan da Tanzania da Pakistan da Papua New Guinea da Pakistan da Yemen da sauransu," in ji sanarwar ta UNICEF.
Hawkins ya kara da cewa a shekarar da ta wuce, gwamnatin Najeriya da hadin gwiwar UNICEF sun yi nazari kan wannan matsalar kuma an samu sauyi da taimakon ma'aikatar ruwa ta kasar da hadin gwiwar abokan hulda da ke sa ido kan wannan fannin.
Sai dai ya ce ana bukatar sa ido domin ganin irin shirin ya dore, da zage damtse wajen samar da tsaftataccen ruwan sha, sakamakon yadda hakan ya zama gagarumar matsala ba ga yara ba har da al'ummar Najeriya, inda kashi 86 cikin 100 na 'yan kasar ke fama da matsalar, wadanda suke samun ruwan kuma ba shi da tsaftar da za a yi amfani da shi.
A karshe UNICEF ya ce matukar aka ci gaba da tafiya kan wannan tsarin, kasar za ta kasa ciki muradun ƙarni da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya a gaba, kuma samun ingantacce kuma tsaftataccen ruwan sha na daga cikinsu.