BBC

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

MenuAfrique
BBC

Rashford zai buga wa United Europa League da Granada

 117876414 Rashford3333 Marcus Rashford na gaida kocin Man United Ole Gunnar Solskjaer

Fri, 9 Apr 2021 Source: BBC

Marcus Rashford zai yi wa Manchester United wasan Europa League da za ta fafata da Granada karawar farko a Quarter final ranar Alhamis.

Rashford mai shekara 23, ya ci kwallo a wasan da Manchester United ta ci Brighton 2-1 a gasar Premier ranar Lahadi, amma aka fitar da shi a kan gadon daukar marasa lafiya.

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer shi ne ya tabbatar da cewar dan kwallon tawagar Ingila ya murmure zai kuma iya buga wasan na ranar Alhamis din.

Shima Juan Mata yana cikin 'yan kwallon da United za ta fuskanci kungiyar Spaniyar har da matashin dan wasa mai shekara 18, Anthony Elanga.

Sai dai Anthony Martial ba zai buga gumurzun ba, sakamakon jinya, shi kuwa Eric Bailly ya kamu da cutar korona shima ba zai yi wasan ba.

Ana sa ran tsohon dan kwallon Tottenham, Roberto Soldado shi ne zai ja ragamar 'yan wasan Granada wadda take ta tara a kan teburin La Liga na bana.

Source: BBC