Real Madrid ta tashi 0-0 tsakaninta da Getafe a karawar mako na 32 a gasar La Liga da suka yi ranar Lahadi.
Da wannan sakamakon Real tana ta biyu da tazarar maki uku tsakaninta da Atletico Madrid wadda ta casa Eibar da ci 5-0.
Real Madrid ta buga wasan ba wasu manyan 'yan kwallonta, sakamakon jinya, wasu kuma sun kamu da cutar korona sun killace kansu.
Barcelona mai kwantan wasa tana ta uku a teburin gasar Spaniya da maki 65 da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid.
Ranar Asabar Barcelona ta lashe kofin farko a bana, inda ta ci Copa del Rey kuma na 31 jumulla, ba wadda ta kai ta yawan cin kofin a tarihi.
Real Madrid wadda ke rike da kofin La Liga ta kai wasan daf da karshe a Champions League, bayan da ta yi waje da Liverpool da ci 3-1 gida da waje.
Real din za ta karbi bakuncin Chelsea a karawar farko a karshen makon nan Afirilu, sannan ta ziyarci Stamford Bridge a karawa ta biyu a gasar Zakarun Turan a farkon makon watan Mayu.