Annobar cututtuka abu ne mai dadadden tarihi a duniya baki daya, domin kuwa za a iya cewa tarihin cututtuka daidai yake da tarihin duniya.
Masu bincike kan cututtuka sun bayyana cewa tun farkon tarihi aka rika samun manyan annoba da suka yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin mutane tare da jefa kasashen duniya cikin rudani.
Ta baya bayan nan dai ita ce annobar cutar korona wacce ta samo asali daga birnin Wuhan na kasar China a watan Disambar shekarar 2019 kuma sannu a hankali ta bazu a kasashen duniya tare hallaka dubban mutane.
Yanzu haka kasashen duniyar na ta fadi tashin ganin sun dakile cutar ta hanyar yi wa al'ummominsu allurar riga-kafi baya da daukar wasu matakan kariya.
Kafin nan ma an sha fama da annobar cutar Ebola a duniya, inda ta kashe mutane da dama a wasu kasashen Afirka a tsakanin 2014 zuwa 2015 kafin a cim mata.
Farfesa Isa Sadiq Abubakar, darakta na cibiyar bincike mai zurfi kan cutukan da ke yaduwa a Jami'ar Bayero Kano ya shaida wa BBC cewa lokaci zuwa lokaci annoba takan bullo, kuma tarihi ya nuna cewa an samu bullar annoba iri daban-daban da ta girgiza duniya ko wani bangare na duniya.
"Misali, shekaru sama da dari da suka wuce akwai annobar cuta mai suna Plague da ta bulla ta kuma yadu a duniya inda kasashen Turai da dama suka sha wahala bayan da ta hallaka kusan rabin al'ummar kasashen Turai a shekarar 1343," in ji shi.
Ya kara da cewa: "Sannan shekaru dari zuwa sama da suka wuce an taba samun barkewar annobar cutar sarkewar numfashi da ake kira "Spanish Flu" da ta yi kama da ta korona don sai da aka rika tilasta wa mutane saka takunkumi."
Baya ga wadannan, a Najeriya akwai annoba da dama da aka yi fama da su musamman a arewacin kasar a shekaru da dama da suka gabata, kuma har a shekarun baya-bayan nan ma wasu na kara tasowa akai-akai.
Farfesa Isa Sadiq Abubakar ya yi wa BBC karin bayani cewa akwai cutattuka masu yaduwa da dama da ba su riga sun zama annobar ba, amma kuma sukan rika barkewa lokaci-lokaci tare da haifar da nakasu ga wadanda ta kama.
Cutar 'Yar Agana "Smallpox"
Akwai su da dama amma cutar 'yar Agana da a Turance ake kira Smallpox wacce aka kawar a shekarar 1976, duniya baki daya kuma ba a sake samun bullar ta ba.
Ita kadai ce a tarihi ta bace ko kuma an kawar da ita baki daya daga doron kasa.
Amma kuma da aka tashi tsaye da daukar matakan allurar riga-kafi shi ya sa aka samu nasara ganin bayansa.
Ta kai tsawon shekara 100 tana damun mutane a duniya tare da kashe mutane da dama, wasu kuma da suka warke za a rika ganin suna da cin zanzana a fuska da jiki wanda da ma shi ne alamun ta.
Takan haifar da matsaloli daban-daban da suka hada da makanta baya ga kisa.
"Kurarraji ne manya-manya kan fito su baibaye jikin wanda ya kamu da cutar 'Yar Agana , baya ga zazzabi mai zafin gaske," in ji farfesa Sadiq.
Kyanda
Kyanda cuta ce da ta fi addabar kananan yara kuma aka dade ana fama da ita a duniya.
Takan kuma zo da tari da zazzabi mai zafi da fesowar kananan jajayen kuraje a jiki.
Farfesa Sadiq ya ce cutar kyanda kan iya zuwa a annoba, amma saboda takan dauki wani lokaci kafin ta bulla, musamman ma a lokacin da iska ke kadawa amma kuma yanzu abin ya lafa ba kamar a baya da take kama kananan yara da dama ta kuma hallaka su ba.
"Ga wanda ya yi shekaru kadan a duniya ya san cewa yara kanana da akan haifa sukan rika mutuwa, amma da aka fara daukar matakan riga-kafi daban-daban ga kananan yara ya rage yaduwar ta," in ji farfesa.
Ya ce: "Daga baya duk kasashen duniya kusan sun shawo kanta, sai dai har yanzu a Najeriya musamman yankin arewaci, tana ci gaba da tasowa lokaci zuwa lokaci."
Sankarau
Farfesa Isa Sadiq ya ce cutar sankarau ta dade tana addabar al'ummar Najeriya musamman ma a arewacin kasar.
Kuma ya ce akan samu sankarau ta annoba musamman idan iskar hunturu na kadawa, takan yada ta har zuwa lokacin zafi da takan karu, da kan sa wasu ke danganta ta da iskokai, kuma ba yara kadai take kama wa ba har da manya.
Masana sun bayyana cewa ko a shekarun 1996 da 1997 annobar sankarau ta yi munin da sai da ta hallaka mutum 11,000 a jihar Kano da ke arewacin kasar kawai.
Farfesa Isa Sadiq ya kara da cewa "A da idan aka yi annobar da ta dauki ran mutane da yawa sai kuma ta lafa sai bayan wasu shekarun, amma dai tun daga 1996 ba a kara samun mummunar annobar sankarau ba sai wajen 2015."
"Tana zuwa da zazzabi, da ciwon kai da kuma jijjigar jiki sannan jiki yana sankarewa," a cewarsa.
Baya ga kisa da sankarau ke yi, Farfesa Isa, ya ce tana nakasa wadanda suka kamu da ita, ta makantar ta kurmantar ko ta bata kwakwalwar wasu.
Shekaru da dama da suka wuce an samu riga-kafi mai inganci wanda gwamnati lokaci-lokaci na fitowa tana kaddamar da allurar riga-kafin
Ya kuma ce yanzu ta yi sauki ne saboda shekaru da dama da suka wuce gwamnati tana fitowa lokaci-lokaci tana fadakarwa ka mutane su fit a yi musu allurar rigakai na sankarau, ahakan ya sa an samu raguwarta a wurare da dama.
"Riga-kafi abu ne mai matukar muhimmanci a cikin matakai na kariya da ake dauka, yana gaba-gaba tare da kuma tsafta, amma rigakafi shi ne kan gaba don shi ne ya ke kawo nasararoin kawar da cuattuka masu yaduwa ko kuma anona,'' in ji farfesa.
Amai da gudawa ko kwalara
Duk da cewa cutar amai da gudawa ko kwalara kamar yadda farfesa Sadiq ya bayyana ba ta cikin cututtukan da za a iya kiran ta annoba, amma a wasu lokutan takan zamo annobar a wuraren da ta barke saboda rashin kula da tsaftace muhalli.
Farfesa Isa ya ce "An fi samun ta a lokacin rani idan ruwa ko abinci ya gurbata, kana tana zuwa ne daga lokaci zuwa lokaci."
Ya kuma ce kasashen duniya sun dade da dakile cutar ta kwalara, amma a kasashen masu tasowa kamar Najeriya takan zo a lokaci zuwa lokaci.
Sai dai kuma an samu raguwa sosai saboda matakan da gwamnati ta dauka na riga-kafi da kuma fadakarwa game da tsaftar muhalli da abinci.
Tasirin alluran riga-kafi
Kamar yadda bayanai suka nuna game da yadda aka samu nasarar kawar da wasu annoba a shekarun baya, haka batun yake yanzu ma in ji cewa farfesa Isa Sadiq.
Ya ce muddin an son kawar da annobar cutar korona sai an bi hanyar da aka bi a baya wajen kawar da sauran annobar kamar su Spanish Flu da Flague da makamantansu a fadin duniya.
"Riga-kafi abu ne mai muhimmanci a cikin matakai na kariya da ake dauka, tare da tsafta da cin abinci masu inganci, amma gaskiyar magana riga-kafi shi ne kan gaba idan ana maganar samnun nasarorin kawar da annoba ne, a cewarsa.
Don haka ya ce allura riga-kafin cutar korona da yanzu haka ake ta takaddama a wasu wuraren game da sahihancinta, idan aka yi la'akari da abubuwan da suka faru a baya na annobar, an samu nasara ne ta hanyar yin allurar riga-kafin.
Ya kara da cewa: "Akwai tarihin nasarar allurar riga-kafin annoba masu kama da korona da aka samu, don haka babu wata matsala idan aka ce an yi na korona din.
"Idan kika duba yanzu haka a kasar Isra'ila da suka dage da yi wa mutane allurar riga-kafin, yanzu haka an samu raguwar yawan mutanen da suke kamuwa da kuma mutuwa sosai a kasar," in ji shi.