Menu

Rikicin Chadi: Anyi zanga zangar adawa da gwamnatin Mahamat Deby

 118214567 5ef945fa 6d74 4f79 Ae31 926600624523 Zanga zanga ta barke a Chadi, inda al'umma ke buƙatar a rusa majalisar sojin ƙasar

Wed, 28 Apr 2021 Source: BBC

Zanga zanga ta barke a Chadi, inda al'umma ke buƙatar a rusa majalisar sojin ƙasar da Janar Mahamat Idriss Deby ke jagoranta.

Janar Mahamat mai shekaru 37 ɗan tsohon shugaba marigayi Idris Deby Itno ne, kuma an naɗa shi ne bayan kashe mahaifinsa yayin gumurzu da ƴan tawaye.

Jagororin adawa da kungiyoyin masu fafutuka sun ce za su ci gaba da zaman dirshen kan tituna matsawar ba a saurare su ba.

Amma rahotanni sun nuna cewa hukumomi sun shirya yin fito-na-fito da masu zanga zangar.

Shugabannin adawa ne suka kira zanga-zangar a ranar Talata.

Wani ɗan jarida a ƙasar Bello Bakary Mana ya wallafa bidiyon zanga-zangar.



An riƙa ƙona tayu da tutar Faransa a fadin N'Djamena. Kuma bukatar masu boren ita ce a rusa majalisar soji da ke mulkin ƙasar.

Suna kuma bukatar a zauna kan teburin tattauna batun gudanar da ingantaccen zaɓe.

Kafafen yaɗa labaran cikin gida sun ce an kashe mutun daya an kuma raunata wasu da dama, yayin da sojoji ke amfani da ƙarfi kan masu boren.

Al'umma a N'Djamena sun ce sun shaida yadda ƴan sandan kwantar da tarzoma ke shiga gida gida neman masu zanga zanga.

Kazalika an katse intanet da nufin takaita bayanai da ke fita.

A yanzu dai ana fargabar Chad za ta iya faɗawa cikin wani sabon rikicin basasa.

Dama kuma tana fuskantar ƴan tawaye da ke tunkarowa daga arewaci, wadanda suka sha alwashin kifar da gwamnatin soji da ta karɓi mulki.

A baya ƙungiyar ƴan tawayen ta Front for Alternation and Concord a Chad ta buƙaci tattaunawa da sojojin, amma majalisar sojin ta yi watsi da buƙatar.

Alƙawalin tattaunawa

Sabon shugaban Chadi Mahamat "Kaka" Déby Itno ya gabatar da jawabi ga ƴan ƙasar Chadi inda ya yi alƙawalin tattaunawa da nufin dawo da ƙasar kan mulkin dimokuraɗiyya cikin watanni 18, bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Déby.

Sabon shugaban kuma ya yi alƙawalin yaƙi da ta'addanci.

Jawabinsa na zuwa yayin da zanga-zanga ta ɓarke a N'Djamena fadar gwamnatin Chadi da kuma Moundou a kudancin ƙasar kan adawa da mulkin soja.

Source: BBC