Menu

Rikicin Chadi: Wasu 'yan adawa sun shiga gwamnatin mulkin sojin kasar

 118303492 Mediaitem118303491 Mahamat Deby Itno ne ke jagoran gwamnatin rikon kwarya

Tue, 4 May 2021 Source: BBC

Majalisar Sojin kasar Chadi ta sanar da kafa gwamnatin rikon kwarya, wadda ta hada da wasu 'yan adawa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar sojin, Azem Bermandoa Agouna, ya karanta a gidan talbijin na kasar ranar Lahadi, ya ce majalisar za ta kunshi mabobi 40.

Azem Agouna ya sanar da kirkirar ma'aikatar sulhunta 'yan kasar, wadda Acheick Ibn Oumar, tsohon shugaban 'yan tawaye kuma tsohon mai ba da shawara ga marigayi Shugaba Idriss Deby, zai jagoranta.

An bayar da mukaman ministoci biyu ga mambobin kungiyar 'yan tawaye ta National Union for Democracy and Renewal (UNDR).

Shugaban UNDR Saleh Kebzabo ya yi maraba da sabuwar gwamnatin, yana mai cewa "ta soma dauki harama ta yadda za mu yi aiki", kamar yadda gidan rediyon Faransa na RFI ya ambato shi yana fada.

Sai dai ba a sanya jam'iyyar adawa ta Transformers party da Succes Masra yake jagoranta ba.

Janar Souleyman Abakar Adoum, daya daga cikin mambobi 15 majalisar sojin, ya samu mukamin ministan tsaron al'umma.

Kazalika wani shugaban 'yan tawayen, Mahamat Ahmat Alhabo, zai kasance ministan shari'a a sabuwar gwamnatin.

Shugabannin riko na majalisar sojin, wadanda Mahamat Idriss Deby ke jagoranta, sun sha alwashib maido da mulkin dimokradiyya cikin wata 18.

Source: BBC