Menu

Rikicin Isra'ila da Falasɗinawa: Su wane ne Larabawan Israila?

 118493926 53bcb0fb D9ef 4701 Ab5c 450d011b2b7d Su ne Larabawa 'yan tsiraru, waɗanda asalinsu Falasɗinawa ne amma kuma 'yan ƙasar Isra'ila ne

Fri, 14 May 2021 Source: BBC

Wannan makon ya kasance mai cike da rikici a yankunan Isra'ila da Falasɗin.

Bayan shafe kwanaki ana tashin hankali, Isra'ila ta saka dokar ta-ɓaci a birnin Lod da ke tsakiyar ƙasar, a kusa da Tel Aviv babban birnin ƙasar, bayan Larabawan birnin sun yi zanga-zanga.

Wannan ne karon farko da gwamnatin Isra'ila ke saka dokar ta-ɓaci a kan Larabawa tun bayan shekarar 1966.

To, su wane ne Larabawa Isra'ila?

Tarihin Larabawa 'yan Isra'ila

Babu mamaki kuna jin ana cewa Isra'ila ƙasar Yahudawa ce, amma akwai waɗanda ba Yahudawa ba ma.

Su ne Larabawa 'yan tsiraru, waɗanda asalinsu Falasɗinawa ne amma kuma 'yan ƙasar Isra'ila ne.

Al'ummar Isra'ila sun kai kamar miliyan tara, kuma kusan ɗaya cikin biyar nasu - wato kusan miliyan 1.9 - Larabawa ne.

Falasɗinawa ne waɗanda suka ci gaba da zama a cikin Isra'ila bayan ƙirƙirar ƙasar a shekarar 1948, yayin da 750,000 daga cikinsu ko dai suka gudu ko kuma aka ƙwace gidajensu bayan ɓarkewar yaƙin da ya biyo baya.

Waɗanda suka tsere sun matsa gaba da iyakar ƙasar zuwa Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gaza da kuma sansanonin 'yan gudun hijira a yankin.

Sauran da suka rage a cikin Isra'ila suna kiran kansu Larabawan Isra'ila ko Falasɗinawan Isra'ila ko kuma Falasɗinawa kawai.

Larabawan Isra'ila akasarinsu Musulmai ne amma kamar sauran yankunan Falasɗinu, Kiristoci ne suke biye musu a yawa.

Tun daga zaɓen farko da aka yi a ƙasar aka bai wa Larabawan 'yancin zaɓe ranar 25 ga watan Janairun 1949 - sai dai sun ce ana yawan nuna musu wariya a ƙasar tsawon shekaru.

Haɗewa

Larabawa da Yahudawan Isra'ila ba su fiya yin mu'amala ba, duk da cewa annobar korona ta sa sun yi aiki tare.

Ɗaya daga cikin hanyoyin da ke haɗa su ita ce ɓangaren lafiya - inda Larabawan da Yahudawan ke haɗuwa a asibiti ɗaya da magani ɗaya da likita ɗaya.

Kashi 20 cikin 100 na likitocin Isra'ila Larabawa ne, su ne kashi 25 na ma'aikatan jinya, su ne kashi 50 na masanan kimiyyar haɗa magunguna.

Sai dai abu ne mai wuya a iya gane alaƙa tsakanin mutanen biyu duk da cewa 'yan ƙasa ɗaya ne.

Misali, rundunar soja na taka muhimmiyar rawa a Isra'ila sannan kuma shiga horon soja wajibi ne ga 'yan ƙasa.

Amma kuma horon bai zama dole a kan Larabawa.

Nuna wariya

Larabawan Isra'ila sun sha bayyana cewa ana nuna musu wariya a cikin ƙasarsu, kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da da yawa sun gasgata hakan.

Amnesty International ta ce Isra'ila ta ayyana wariya kan Falasɗinawa da ke zaune a ƙasar a hukumance.

Wani rahoto da Human Rights Watch ta fiatar a Afrilun 2021 ya ce gwamnatin Isra'ila ta masu wariya ce, wadda ke aikata laifukan take haƙƙi kan Larabawan Isra'ila da kuma Falasɗinawa da ke zaune a garuruwan da ta mamaye a Yammcin Kogin Jordan da kuma Gaza.

Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta yi watsi da rahoton tana cewa "na ƙarya ne".

Larabawan na cewa gwamnati na da tsohon tarihin ƙwace musu filaye tare da zargin Yahudawa da nuna musu wariya a kasafin kuɗi da ayyukan ƙasa.

Su ma dokokin da aka kafa wa kowane rukuni sun sha bamban a ƙasar.

'Saniyar ware'

Misali, dokokin Isra'ila na samun takardar shaidar zama ɗan ƙasa sun fi wa Yahudawa alfarma, waɗanda nan take za su iya samun fasfo ba tare da duba daga inda suka fito ba.

Su kuma Falasɗinawa da aka kora da yaransu ba su da wannan 'yancin.

A 2018, majalisar dokokin Isra'ila ta amince da wata doka da ke haramta amfani da Larabci a matsayin harshen ƙasa - da kuma Hebrew - sannan suka ayyana 'yancin samar da yanayi na ƙashin kai "na musamman ga Yahudawa".

Ayman Odeh, wani Balarabe kuma ɗan majalisa, ya ce Isra'ila ta ƙaddamar da dokar 'ɗaukaka Yahudawa', yana mai faɗa wa Larabawa cewa 'saniyar ware za su zama a koyaushe a Isra'ila.'

A gefe guda kuma, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi alƙawarin samar da daidaito amma ya ce "masu rinjaye ne za su yanke hukunci".

Source: BBC