Menu

Rikicin Isra'ila da Falasɗinawa: Ƙarfi da kuma gazawar makaman da ƙungiyar Hamas ke yaƙar Isra'ila da su

 118481389 Gettyimages 593234900 Hamas na da makaman da za su iya kai hari a biranen Tel Aviv da na Ƙudus, inji masana

Fri, 14 May 2021 Source: BBC

Yayin da mutuwa da wahalhalu sun shafi dukkan bangarori biyu da ya dade da barkewa tsakanin kungiyoyin Falasdinawa masu dauke da makamai a Zirin Gaza da dakarun Isra'ila, wannan gwagwarmayar ta kasance wadda ba a san inda za ta kare ba.

Isra'ila ce kan gaba nesa ba kusa ba a bangaren kayan yaki na sama kamar jiragen yaki da jiragen maras matuki da za ta iya amfani da su wajen kai hare-hare a Gaza a duk lokacin da ta so.

Amma duk da cewa ana kallon Hamas da Islamic Jihad a matsayin wadanda aka fi karfinsu, sun mallaki isassun makaman yakin da za su iya kai wa Isra'ila hari. Sun ma gwada wasu dabaru. Dakarun Isra'ila sun harbo wani jirgi maras matuki - wanda ba shakka yana dauke da makami - da ke kan hanyarsa ta shiga Isra'ila daga Gaza.

Wani kakakin ma'aikatar tsaro ta Israila ya ce "wasu zaratan sojojin Hamas" sun so kutsawa Isra'ila ta ani rami da su ka haka daga yankin kudancin Zirin. Da alama Isra'ila ta sami labarin harin, kuma "ta rusa" ramin.

Amma makaman da Falasdinawa su ka mallaka mafi muhimmanci su ne na rokoki masu linzami iri-iri da ake iya harbawa daga kasa zuwa duk wani wuri a cikin Isra'ila. Cikinsu (tare da wasu makaman kamar Kornet mai iya fasa tankar yaki), ana tsammanin an yo fasa-kwaurinsu ne daga Masar ta hanyar wasu ramukan karkashin kasa da ta hada Gaza da yankin Sinai na Masar.

Amma yawancin makaman a cikin Gaza ake hada su, inda Hamas da Islamic Jihad ke da masana'antun da ke keras su. Israila da wasu masana na kasar waje na tsammanin Iran na da hannu wajen samar da kwarewar da kungiyoyin na cikin Gaza ke da shi.

Iya sanin ainhin yawan makaman da Hamas ta mallaka abu ne da ba zai yiwuwa ba.

Amma ta na da dubban makai masu tasiri iri-iri. A fili ya ke cewa Isra'ila na da masaniya kan batun amma ba ta son cewa uffan. Abin da kakakin ma'aikatar tsaro na Isra'ila ya iya cewa shi ne Hamas na iya ci gaba da kai wadannan hare-haren na "wani lokaci mai tsawon gaske."

Hamas na da tarin rokoki, a misali tana da masu gajeren zango kamar Qassam (mai iya kai nisan kilomita 10) da na Qudus 101 (mai kai wa kilomita 16); da irin na Grad (kilomita 55); da na Sejil 55 (kilomita 55).

Amma Hamas na da wasu rokokin kamar M-75 (kilomita 75); da na Fajr (kilomita 100); da na R-160 (kilomita 120); da wasu rokokin kirar M-302 da ka iya kai nisan kilomita 200.

A bayyane ya ke cewa Hamas na da makaman da za su iya kai hari a biranen Tel Aviv da na Ƙudus, kuma za su iya kai wa har yankin gabar tekun kasar, yankin da yawancin al'ummar Isra'ila su ke, ban da muhimman gine-gine da ofisoshin gwamnati.

Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta ce cikin rokoki fiye da 1,000 da aka harba cikin Isra'ila a kwanaki ukun da su ka gabata, kimanin 200 ba su fice daga Zirin na Gaza ba.

Ma'aikatar ta kuma ce na'urar "Iron Dome" ta yi nasarar kakkabo kashi 90 cikin 100 na rokokin da su ka isa Isra'ila. Amma an sami tangarda a birnin Ashkelon, inda rokokin su ka yi barna domin na'urar ba ta aiki, wanda ke tabbatar da na'urar na da iyakar aikin da za ta iya yi amma ba za a iya cewa za ta kare kasar ba daga hare-haren roka daha Gaza ko kuma wani wurin na daban.

Wannan rikicin harba wa juna makamai da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa tsakanin Isra'ila da Falasdinawa ba zai haifar wa kowa alheri ba.

Sai dai ganin cewa kasashen Larabawa na kulla yarjejniyoyin zaman lafiya da Isra'ila, kuma har yanzu Falasdinawa kawunasu a rabe su ke, da wuya a iya hango mafita daga wannan rikicin nan kusa.

Jonathan Marcus shi ne wakilin BBC mai nazarin dangantaka tsakanin kasashe da harkokin waje da batutuwan tsaro da na diflomasiyya.

Source: BBC