Jam'iyyar PDP reshen jihar Kano ta ce ta kai ƙorafi gaban uwar jam'iyyarsu kan yadda gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ke kokarin kawo rikici wajen zabar mataimakin shugaban jam'iyyar reshen arewa maso yamma.
PDPn Kano ta zargi Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da ƙoƙarin haifar da ruɗani, da yi musu yankan-baya da kuma yunƙurin hana su damar da aka bai wa kowacce jiha a shiyyar kamar yadda wani taron jagororin arewa maso yamma ya amince kwana guda kafin babban taron.
A cewarta Aminu Tambuwal ya saya wa wani ɗan takara daga Kano takardun neman kujerar mataimakin shugaban PDP shiyyar arewa maso yamma da kuma dagewa kan lallai sai an yi zaɓe bayan kowacce jiha ta amince da masalaha wajen fitar da duk kujerun da aka keɓe mata.
Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, tsohon dan takarar mataimakin gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Kano, ya bayyana wa BBC Hausa cewa suna da kwararan shaidu da suka tabbatar musu da cewa gwamnan na Sokoto ne ke shirya wannan makarkashiya a gare su, saboda wata manufa da yake da ita a nan gaba.
''Mu wannan ya zama cin fuska garemu, domin an cimma matsaya tun farko dangane da wannan batu, kuma mu a baya mun dauka cewa wannan magana jita-jita ce, amma sai ta bayyana cewa gaskiya ce'', in ji Aminu Abdussalam.
Abin da uwar jam'iyyar ta kasa ta ce
Sanata Umar Ibrahim Tsauri, shi ne sakataren jam'iyyar PDP na Najeriya, ya kuma shaida wa BBC cewa tun kusan wata shida da suka wuce aka bayar da takardu (fom) na duk dan takarar da ke akwai na kujerun arewa maso yamma, amma daga baya sai Kwankwaso ya ce Tambuwal ya saya wa wani fom don ya yi takara.
''Ina zaune a Ofis sai aka ce min wani ya zo ya sayi fom ma wani dan takara, da na bincika sai aka ce Tambuwal ne ya saya wa wani, sai na kira shi, yace min tsakaninsa d Allah bai san an saya ba'', in ji Sanata Tsauri.
Ya ƙara da cewa ko lokacin da suka zauna suka yi wata ganawa a Kaduna, Kwankwaso ya tayar da maganar, kuma Tambuwal ya jaddada cewa shi bai saya wa kowa fom ba.
Sakataren na PDP na ƙasa ya ƙara da cewa: ''Tun da jam'iyya ta kawo dan takara kuma an amince da shi an ce a je a yi shi, amma tunda shi wancan ya sayi fom, ka ga ai ba zaka hana shi yin takara ba''
Ya ce ko a jihar Kaduna ma an samu irin wannan, inda 'yan jam'iyya suka bayar da sunan mutum guda amma wani ya ce bai yarda ba, sai aka ce ya je ya sayi fom ya shiga takara.