Menu

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe sojoji 11 a jihar Benue

 117894800 F9c8bb46 2dd9 4659 Bd3f E8b0933470c8 Shugaban sojojin Najeriya Laftanal Janar Ibrahim Attahiru

Sat, 10 Apr 2021 Source: BBC

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojojinta 11 a jihar Benue.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Birgediya Muhammad Yerima ya aike wa manema labarai, ta ce sojoji goma da jami'in tsaro daya ne suka mutu, wadanda a baya ake nema sakamakon ɓatan da suka yi, har aka aike da tawagar hadin gwiwa domin nemo su.

Sai dai tawagar ta samu gawar sojojin a karamar hukumar Konshisha da ke jihar Benue.

Sai dai rundunar sojin ba ta bayyana wani abu game da waɗanda ake zargi da kisan sojojin ko wani abu da ya yi silar ajalinsu nasu ba.

"A yayin da aka yi gaggawar kwashe gawarwakin, ana kuma kokarin gano wadanda suka aikata mummunan aikin domin hukunta su," in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa: "Sojojin Najeriyar karkashin jagorancin Laftanal Janar Ibrahim Attahiru na ci gaba da kokarin ganin zaman lafiya ya inganta, da kawo karshen bata gari a kasar baki daya."

Birgediya Yerima ya ce an umarci jami'an tsaro da ke yankin su zage damtse don daukar mataki kan masu barazana ga tsaro a jihar.

A karshe sanarwar ta buƙaci farar hula su bai wa jami'an tsaro hadin kai, da kai rahoton duk wani abu da bai kwanta musu a rai ba, da taimaka wa wajen kama ɓata gari.

Jihar Biniwai ta yi ƙaurin suna wajen samun tashe-tashen hankula da suka haɗa da na ƴan fashi da rikicin manoma da makiyaya, amma a baya-bayan nan an ɗan samu zaman lafiya a yankin.

Birgediya Yerima ya tabbatar wa da mazauna yankin cewa wannan kisa da aka yi wa rundunar sojin ba zai shafi zaman lafiyar da fararen hula ke ciki ba.

Benue na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

Ko a ranar 20 ga watan Maris ɗin da ya gabbata ma wasu 'yan bindiga sun kai wa tawagar Gwamna Samuel Ortom na Benue hari a gidan gonarsa da ke kan hanyar Makurdi zuwa Gboko.

Jami'an da ke tsaron gwamnan sun yi musayar wuta da maharan yayin da tawagarsa ke kan hanyar komawa gida daga Gboko.

Source: BBC