Yardarki na da muhimmanci a garemu. Wannan na nufin cewa BBC ta ɗaura ɗamarar kare bayananki. Yana da muhimmanci ki karanta wannan sanarwar don sanin yadda muke amfani da bayananki da kuma dalilin da ya sa muke amfani da su.
Wannan sanarwa ta kunshi yadda muke karɓa da amfani da bayananki a yayin da kuma bayan mu'amalarki da mu, kamar yadda dokar tsare sirri ta tanada.
Abin da ya sa muke karɓar bayananki da kuma yadda za ki shiga
Hikayata gasa ce ta ƙagaggun gajerun labarai wadda ke samar da dama ga mata marubuta, waɗanda ba su ƙware ba da kuma ƙwararru, don nuna fasaharsu da ba da damar karanta labaransu a harshen Hausa. Dole ne labaran da za a shiga su kasance ƙagaggun labarai kan wani jigo.
Mata biyu na iya haɗa gwiwa su shigar da labari guda amma ka da su haura mata biyu, kuma labari ɗaya kacal mace za ta iya shigarwa. Wata tawagar alƙalai waɗanda ba ma'aikatan BBC ba ne, da ta ƙunshi malaman jami'a za su zaɓi gwarzuwa ɗaya da labarinta ya yi nasarar yin na ɗaya sannan za su zaɓi ta biyu da ta uku.
Kafin tura wa alƙalan labaran don tantancewa za a cire duk wani bayani dangane da mai shiga gasa kuma ba za a aika masu ko wane irin bayani kan masu shiga gasar ba.
Waɗanda su ka yi nasara za su samu kyautar kuɗi da lambar yabo: wannan ya ƙunshi $2,000 ga wadda ta zo ta ɗaya, $1,000 ga wadda ta zo ta biyu, $500 ga wadda ta zo ta uku.
BBC za ta watsa labarai 12 da alƙalan suka ce sun cancanci yabo da guda ukun da suka yi nasara a tasharta ta BBC Hausa. Duka labaran da aka naɗa za su ƙunshi sunan labarin da sunan marubuciyar.
Ma'aikatan BBC Hausa za su karanta labaran da suka cancanci yabo cikin mako 12. Waɗanda suka yi nasara za su karanta labarinsu gaba ɗaya da kansu a ɗakin gabatar da shirye-shirye na BBC.
Za a watsa karatun labaran da aka naɗa a tashar BBC Hausa da tashoshin rediyo na abokan hulɗarmu Freedom Rediyo da Rediyo Gotel da Rima Rediyo da ma wasu.
Za a wallafa kuma a watsa muryoyin marubutan da labaransu suka yi nasara a gasar da aka naɗa da sunan marubutan, a shafin BBC Hausa na intanet da BBC Hausa Rediyo da shafukan sada zumunta na BBC kamar Twitter da Instagram da Facebook.
BBC ka iya gayyatar waɗanda suka yi nasara da wasu waɗanda labaransu suka cancanci yabo, domin halartar taron bayar da kyaututtuka a Abuja. BBC za ta ɗauki nauyin kuɗin mota da masauki wanda bai wuce ƙima ba. Waɗanda aka gayyata su ne ke da alhakin nema wa kansu izinin shiga Najeriya.
Tawagar BBC Hausa za ta karɓi bayananku don Gasar Gajerun Ƙagaggun Labarai ta Mata.
Tawagar BBC Hausa za ta amsa bayanaku ta adireshin email da shafin inatnet da BBC ke amfani da shi. Idan muka watsa labarinki, yana iya kasancewa a shirye-shiryen da ake adanawa a intanet kuma ana iya amfani da labarin naki a shirye-shiryenmu na gaba.
Me muke karɓa kuma ta yaya za mu yi amfani da shi?
Sai shekarunki sun kai 18 ko sun haura za ki iya shiga gasar. BBC za ta karɓa kuma ta yi aiki da bayanan da suka shafe ki waɗanda kika aiko mana. Dole ne a aika duka labarai zuwa: labari.bbchausa@bbc.co.uk kuma dole ya ƙunshi waɗannan bayanan kan marubuciya/marubuta:
Muna tabbatar da cewa shafin da za mu yi amfani da shi yana da ƙa'idojin da suka dace wanda zai tabbatar da cewa ba za su iya yin komai da bayananki ba sai idan mun ba su umarnin yin haka.
Ba za mu yaɗa bayananki da wani ko wasu ba har sai idan doka ta ba mu izinin yin haka.
Adana bayananki
Idan labarin da kika aiko bai yi nasara ba, BBC za ta adana bayananki da abin da kika aiki har tsawon wata shida daga ranar da kika ɗora bayanan, daga nan kuma za a goge shi.
Idan aka sanya labarinki cikin waɗanda suka kai mataki na gaba ko kuma ke ce kika yi nasara, za mu adana bayananki har tsawon shekara biyu bayan an rufe gasar.
Idan kika kai mataki na gaba ko kuma ke ce tauraruwar gasar, sannan muka wallafa labarinki tare da sunanki, to BBC za ta adana bayananki har abada saboda dalilai na aiki. Za a adana bayananki a tarayyar Turai da Birtaniya da Amurka.
Haƙƙoƙinki da ƙarin bayanai
Kina da haƙƙoƙi ƙarƙashin dokokin kare bayanai. Za ki iya neman kwafin bayananki da BBC ta adana.
Kina da ƴanci ki nemi a goge bayananki da muka karɓa sai dai akwai iyakoki da togaciya kan wannan ƴancin, abin da zai sa BBC ta ki amincewa da buƙatarki.
A wasu lokutan, kina da ƴanci ko taƙaita ci gaba da amfani da bayaninki ko ki nuna rashin amincewa da ci gaba da neman bayananki.
Kina da ƴancin ki nemi mu tura miki bayananki ko wata hukumar, a wasu lokutan.
Za ki iya tuntubar Ofishin Kare Bayanai a dataprotection.officer@bbc.co.uk idan kina da tambaya, idan kuma kina so ki samu ƙarin bayanai a kan ƴancinki, ziyarci sashin Bayanan Sirri na BBC da Ka'idojin Kare Bayanai a http://www.bbc.co.uk/privacy
Idan kina da wata damuwa kan yadda BBC take mu'amala da bayananki na sirri, za ki iya bayyana damuwarki da hukumomin da suke sa ido a Birtaniya, wato Ofishin Kula da Bayanai (ICO) https://ico.org.uk/.
Sanarwa kan sabunta wadannan bayanai
Za mu sabunta waɗannan bayanai idan akwai gagarumin sauyi kan yadda muke amfani da bayananki.