Menu

Saudiyya, Iran da Masar na sahun gaba a kasashen da suka fi aiwatar da hukuncin kisa a 2020

 118134332 Gettyimages 1229004769 Amnesty su ce Oman, Qatar da Indiya kuma sun dawo da aiwatar da hukuncin kisa

Thu, 22 Apr 2021 Source: BBC

Ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ne kan gaba wajen aiwatar da hukuncin kisa a duniya cikin shekarar 2020.

Kamar yadda rahoton kungiyar ya bayyana, kasashen Iran da Masar da Iraqi da kuma Saudiyya su ne kashi 88 bisa 100 na rahotannin aiwatar da hukuncin kisa 483 a fadin duniya.

Ta zarge su da nuna ''rashin tausayi da halin ko-in -kula'' a yayin da akasarin kasashen duniya suka mayar da hankulansu wajen ceton rayukan al'ummarsu daga mummunar kwayar cuta.

Jimillar duka rahotonnin a fadin duniya mafi kankanta ne a cikin shekaru goma, amma bai hada kasar China ba.

An yi amannar cewa ƙasar China na aiwatar da hukuncin kisa kan dubban mutane a ko wace shekara, amma kundin bayanan hukuncin kisan da ta ke amfani da shi ya kasance cikin sirrin kasar ne.

Haka ma rashin bayanai a kasashen Korea ta Arewa da Vietnam ya hana ruwa gudu wajen bincikar rahotonni daga wadannan kasashe.

Hukuncin kisa 483 da aka aiwatar a kasashe 18 da aka bayar da rahoto a shekarar 2020 ya yi nuni da raguwa da kashi 26 bisa dari idan aka kwatanta da 657 a shekarar 2019, sannan ya yi kasa da kashi 70 bisa dari daga karuwar da ya yi na hukncin kisa 1,634 da aka aiwatar a shekarar 2015, a cewar rahoton na Amnesty.

A yankin Gabas ta Tsakiya, daukacin adadin ya yi kasa daga 579 a shekarar 2019 zuwa 437 a shekarar 2020.

Hakan na faruwa ne saboda raguwar kashi 85 bisa dari na hukuncin kisan da aka aiwatar a kasar Saudiyya inda aka aiwatar da kisa 27 yayin da aka samu raguwar kashi 50 cikin 100 na yawan aiwatar da hukuncin kisa Iraqi da ta aiwatar da kisa 45.

Amma kuma, rahoton ya bayyana cewa karuwar kashi 300 bisa dari na kisan a kasar Masar ya mamaye raguwar da aka samu a wasu kasashen, inda aka aiwatar da hukincin kisa kan mutane 107 da ya sa ta zama ta uku a kasashen da suka fi yawan aiwatar da hukuncin kisa a duniya.

Ashirin da uku daga cikin mutanen an yanke musu hukuncin ne a bisa dalilan aikata laifukan da suka shafi rikicin siyasa, wanda kungiyar Amnesty din ta ce mummunan rashin adalci ne aka aikata a shari'ar da aka yi amfani da karfin iko wajen tursasa wa mutanen.

Akwai kuma karuwa a aiwatar da hukuncin kisa 57 cikin watannin Oktoba da Nuwamba, bayan yunkurin fasa gidan yarin al-Aqrab da bai samu nasara ba, wanda jami'an 'yan sanda da fursunoni da dama da aka yanke wa hukuncin kisa suka rasa rayukansu.

Kasar Iran wacce ta aiwatar da hukincin kisa 246 ta ci gaba da kasancewa ta biyu a duniya bayan kasar China.

Kungiyar Amnesty ta ce mahukuntan kasar Iran na ci gaba da amfani da hukuncin kisa a matsayin ''wani makami na cimma burin siyasa'' a kan masu zanga-zanga da 'yan adawa, da kuma kananan kabilu.

Sun kuma yanke wa mutane uku hukuncin kisa kan laifukan da suka faru lokacin da suke da shekara 18, wanda ya sabawa dokar kare hakkin biladama ta duniya.

Wata hukuma a kasar Saudiyya ta danganata raguwar da aka samu a aiwatar da hukuncin kisan a can da ''dakatar da hukuncin kisa kan laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi na wucin gadi.''

Amma ta ce Amnesty kila saboda kokarin da kasar ta Saudiyya ke yi wajen kaucewa sukar lamiri kan batutuwan da ke mamaye shugabancinta na kasashe masu karfin tattalin arziki G20.

A Amurka, gwamnatin shugaba Trump ta sake ci gaba da aiwatar da hukuncin kisa bayan tazarar shekaru 17 da aka samu, kuma ta aiwatar da hukuncin kisa kan mutum 10 a cikin kasa da watanni shida.

Kasashen Indiya, da Oman, da Qatar da kuma Taiwan su ma sun dawo da aiwatar da hukuncin kisan.

"Yayin da duniya ke mayar da hankali kan lalubo hanyoyin kare rayukan jama'a daga annobar cutar korona, gwamnatoci da dama sun nuna wani yunkuri marar dadi wajen komawa aiwatar da hukuncin kisa inda suke ta kashe mutane ta halin ko kaka,'' in ji Agnès Callamard, sakatare janar ta kungiyar Amnesty.

"Hukuncin kisa babban abin damuwa ne kuma yin haka a yayin da ake cikin annoba na nuna tsananin rashin tausayawa," in ji ta.

Miss Callamard ta ce mutane da ke jiran a aiwatar da musu da hukuncin kisa sun kasa samun hanyar da za su samu taimako a fannin shari'a daga wadanda ke da aniyar taimaka musu.

"Amfani da hukuncin kisa a cikin wannan hali wani babban laifi ne na cin zarafi da keta hakkin biladama,'' a cewarta.

Source: BBC