Rahatanni daga ƙasar Senegal da ke yankin yammacin Afirka na cewa tarzoma da zanga-zangar 'yan adawa na ci gaba da fantsama zuwa wasu ƙarin jihohin ƙasar.
Bayanai na cew ana ci gaba da bankawa gine ginen gwamnati wuta a jihohin kasar, ciki har da babban birnin Dakar, inda lamarin ya fi ƙamari.
A yanzu lamarin ya isa wasu manyan biranen ƙasar uku, da suka haɗar da Sedhiou da Kolda da kuma Diaoube dukkansu a yankin kudancin ƙasar.
Ganin yadda lamarin ya yi ƙamari tare ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arzikin ta yammacin Afirka, ECOWAS ko kuma CEDEAO ta yi kira kamar sauran kungiyoyin na kasa da kasa da a mayar da takobi kube.
Zuwa yanzu mahukunta sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutane 4, sannan wasu da dama kuma sun jikkata, sakamakon zanga zangar da aka soma a ranar Laraba.
Abin da ya haifar da zanga zangar
Kama dan adawar kasar Ousmane Sonko na jam'iyar MDD wato 'Movement for the Defence of Democracy' da hukumomin ƙasar ta Senegal su ka yi shi ne ummal iba'issan wannan babban hargitsi.
A watan jiya ne aka soma zargin ɗan adawar da yi wa wata ma'aikaciyar otel fyade, yayin da take yi masa tausa, zargin da tuni ya fito ya musanta.
Jam'iyar shi ta MDD ta danganta zargin da wani ƙulumboton siyasa, don hana shi tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar da ake tunkara.
Ana dai sa ran cewar ranar Litanin din nan Sonko zai bayyana a kutu game da zargin da ake mashi.
Wasu bayanai na cewa kiran masu zanga zangar a matsayin 'yan ta'adda da ministan watsa labaran ƙasar ya yi a ranar Jumma'a ya ƙara tunzura masu zanga zangar, inda a yanzu suke kiran shugaba Macky Sall ya sauka ɗungurungum.