Kaftin din Real Madrid Sergio Ramos ba zai buga wasan Liverpool ba a gasar zakatun Turai zagayen kusa da dab da na karshe bayan samun rauni a ƙafarsa.
Ɗan wasan mai shekara 35 ya samu rauni ne wasan da ya buga wa ƙasarsa Spain.
Real za ta fafata ne da Liverpool a ranar Talata, 6 Afrilu da kuma Laraba, 14 Afrilu, kuma a lokacin ne da za fuskanci Barcelona a karawar hamayya ta El Clasico a La Liga.
"Idan akwai abin da na fin jin zafi, shi ne ba zan iya taimaka wa tawaga ta ba manyan wasanni," kamar yadda ɗan wasan ya wallafa a Instagram.
Ramos ya ce ya fahimci ya samu matsala tun a lokacin atisaye bayan wasan da Spain ta doke Kosovo 3-1, kuma bincike ya tabbatar da ya rauni.
Real Madrid ce za ta fara karbar bakuncin Liverpoool.
Hakan ya nuna Ramos ba zai haɗu da Mohamede Salah ba, wanda ya samu rauni a kafadarsa fafatawar da suka yi da Ramos a wasan karshe a shekarar 2018 a Kiev.
Real ce ta lashe wasan da ci 3-1, amma Salah ya ce bai riƙe Ramos ba.
"Duk abin da ya faru zai sauya sakamakon karawar Kiev, kamar yadda ya shaida wa jaridar Marca ta Spain.