Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin dakatar da shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasar, NPA, Hajiya Hadiza Bala Usman daga mukaminta, domin a gudanar da bincike game da wasu kurakurai da ake zargin ta aikata.
An kuma an umarci wani jami'i, Muhammadu Koko, ya rike wannan mukami yaynin da ake gudanar da binciken, wanda wani kwamiti da aka naɗa karkashin jagorancin darakta mai kula da sufurin jiragen ruwan a ma'aikatar sufuri ta kasar, zai gudanar.
Gwamnati ta ce ministan ma'aikatar sufuri ne ya nemi shugaba Buhari ya ba shi izinin kafa kwamitin bincike don ya duba yadda ake gudanar da ayyuka a fanin jiragen ruwa na Najeriya wanda Hadiza Bala Usman ke shugabanta.
Ya kuma ce yayin da ake na wannan bincike ya kamata ta dakatar da ayyukanta har zuwa lokacin da za a kamala bincike.
Kakakin fadar shugaban ƙasa, Garba Shehu ya ce idan Allah ya sa ta wanke kanta bayan an kammala bincike toh shugaban ƙasar zai ba ta izinin komawa bakin aikinta.
''Idan ta wanke kanta toh shugaban kasa zai mata adalci ta koma ta ci gaba da aikinta amma idan akwai kura-kurai da aka gano toh ba'a san abinda zai biyo baya ba''.
Sai dai Garba Shehu bai yi ƙarin haske ba a kan kura-kuran, amma a cewarsa ma'aikatar sufuri na zargin cewa akwai umarni da dama da aka bayar da ba'a aiwatar ba.