Menu

Sirrin kasuwanci: Kuka zai iya taimaka maka wajen cin nasara

 117890991 P09d3nbz Tina Chen mai shekaru 28 ta bayyana kanta a matsayin mai sana'a ita kaɗai

Thu, 29 Apr 2021 Source: BBC

Tina Chen ta yi bayani kan yadda ta ke jajircewa a matsayinta na mace mai sana'a ita kaɗai, da fara sana'a a wata ƙasa.

Tina Chen mai shekaru 28 ta bayyana kanta a matsayin mai sana'a ita kaɗai. Ita ce ta kafa kamfanin HumaniTea, da ke samar da haɗaɗɗen shayi mai madara.

Ta fara kamfanin ne a Landan a watan Disambar 2018 kuma sana'ar ta yi ƙarfi duk da annobar korona. Kwanan nan ta fara sarrafa shayin nata a masana'anta bayan da mutane suka yi mata karo-karo kuma ta sayar da sama da kwalabe 5,000.

A wannan shekarar ta ɗauki mutane biyu aiki ta hanyar tsarin gwamnati na Kickstart scheme.

Amma a yayin haka, ta kusa durƙushewa kuma tana gargaɗin cewa abubuwa na iya wahala musamma idan kai kaɗai ne ka fara sana'ar.

Tina ta yi tunanin fara yin shayin ne daga al'adarta ta Asiya.

An haifi Tina a Taiwan, amma iyalinta sun dawo Los Angeles da zama lokacin tana da shekara huɗu.

A Taiwan iyayenta na shan shayin bubble - wani shayi da ake haɗawa da madara da shayi mai ƙamshi da tafiyoka da ake sha da tsinken shan lemo mai girma - kuma shayin ya yi suna sosai a tsakankanin ƴan Taiwan a California.

Tina ta yi karatu a Jami'ar California, Los Angeles (UCLA), inda ta fara sha'awar yin sana'a - ta yi karatu a fannin kasuwanci sannan ta shiga ƙungiyoyin masu sana'o'i kuma ta yi la'akari da yadda ƙawayenta ke neman karo-karon kuɗi a intanet.

Ta je Landan ta shekara a can ta yi karatu, daga nan sai ta tsunduma son garin kuma ta yi zamanta a can bayan kammala karatun.

A lokacin da take Birtaniya, ta lura akwai gahawa sosai a manyan kantuna, amma babu shayi sosai. Ta yi tunanin ko za ta iya haɗa shayin da ta fi so a lokacin da take yarinya.

Sai ta fara gwaji a ɗakin girkinta na gida.

Tina ta fuskanci dukkanin matsalolin da ake fuskanta na fara sana'a da kanta saboda ita kaɗai ke rayuwa kuma ba ta da dangi a Landan.

"Na nemi wanda za mu fara wannan sana'a tare amma ban samu wanda zai jajirce kamar ni ba," a cewarta.

Tina na haɗawa da sayar da shayinta da kanta, ta kafa rumfuna a wurare kamar kasuwar Borough a tsakiyar Landan.

Sai ta hada ta zuzzuba a kwalabe daga tsakar dare a wani ɗakin girki na haya, sannan ta sayar da su washegari a kasuwanni - ba ta ko samun isashen bacci.

Amma lokacin da take ɗauka tana haɗa shayin ya yi wa jikinta illa inda a wani lokaci ta taɓa ƙonewa da ruwan zafi.

"A lokacin ne na fahimci cewa kula da kai na da matuƙar amfani idan za ka fara sana'a, a cewarta.

Wasu ƙalubalen da ta fuskanta sun haɗa da rikici kan haƙƙin mallakar sunan kamfanin wanda a yanzu ta sauya, da kuma wani lokaci da ta yi odar ganyen shayi amma aka samu tsaiko a isowarsa. Ya ɓata a hanya kuma wannan ya ja ta ɗage ranar ƙaddamar da shayin nata da wata guda.

Wannan na iya damun mutum matuƙa a cewar Tina kuma ta sha zubar da hawaye.

"Amma na fuskanci ashe kuka na taimakawa sosai in ji sanyi a raina."

Ta samu mai ba ta shawara kuma hakan na da matuƙar amfani. Ya ce kar ta fiye damuwa da matsalolinta amma ta mayar da hankali kan mafita.

A yanzu ana sayar da shayinta a shaguna da gidajen cin abinci da dama musamman a Landan.

Tana fatan faɗaɗa ayyukanta ciki har da fitar da shayinta ƙasashen waje yayin da za ta ƙara yawan shayin da take sayarwa a shafinta na intanet.

Tina na ganin cewa yana da amfani masu sana'a su kaɗai kamar ita su samu masu goya masu baya a lokacin da suke cikin matsala.

Ta samu mai ba ta shawarwari a ɓangaren kasuwanci na Babban ɗakin karatu wato British Library Business Centre.

Haka kuma, ta samu ƙawaye irinta masu sana'o'i kuma sun bai wa juna tallafi ta kafar Whatsapp.

Ta koyi ware ranakun ƙarshen mako a matsayin ranakun hutunta, don ta samu lokacin kanta.

"Fara sana'a kai kaɗai akwai kaɗaici amma ba haka ya kamata ba kuma yanzu ba na jin kaɗaici," in ji Tina.

Source: BBC