Menu

Somalia: Ƴan sandan Najeriya 144 sun isa Somalia domin wanzar da zaman lafiya

 118120411 Mediaitem118120410 Tawagar yan sandan Najeriya na Somalia domin aikin wanzar da zaman lafiya

Tue, 20 Apr 2021 Source: BBC

Wata tawagar ƴan sandan Najeriya mai ƙunshe da 'yan sanda 144 ta isa ƙasar Somalia domin aikin wanzar da zaman lafiya.

Tawagar, wadda ke karkashin shirin Tarayyar Afirka na samar da zaman lafiya a Somalia da a takaice ake kira (AMISOM), ta isa kasar ne tun ranar Asabar.

Sanarwar da Tarayyar Afirka ta wallafa a shafinta na intanet ta ce ƴan sandan za su kwashe shekara guda suna aiki a Somalia, wadda ke fama da hare-haren mayakan ƙungiyar Al-Shabaab.

"A shekara ɗayan da za su yi za su bayar da shawarwari da kuma dabaru na aiki ga rundunar ƴan sandan Somaila," in ji sanarwar.

Ta kara da cewa: "Lokacin da suka isa Mogadishu a jirgin sama daga babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, jami'an ma'aikatar lafiyar Somalia sun yi wa ƴan sandan na Najeriya gwaje-gwajen lafiya kamar yadda ake yi domin koauce wa kamuwa da cutar korona inda daga bisani jami'an 'yan sandan AMISOM suka yi musu jawabi.

Babban jami'in ƴan sandan da ke kula da tsare-tsare na AMISOM, Daniel Ali Gwambal ya ce za a tura 'yan sanda 30 zuwa birnin Beletweyne da ke jihar HirShabelle State, yayin da sauran za su gudanar da aiki a matakai daban-daban a birnin Mogadishu.

Ayyukan da ƴan sandan za su yi sun hada da tsaron manyan mutane, atisaye da kuma taimaka wa rundunar ƴan sandan Somalia wajen aikin wayar da kan jama'a, da aikin sintiri tare da 'yan sandan ƙasar da kuma tabbatar da tsaro a wurare na musamman.

Source: BBC