Menu

Spaniya ba ta gayyaci Ramos gasar nahiyar Turai ta bana ba

 118651802 Sergioramosspainsad Sergio Ramos zai kallo gasar turai mei zuwa daga gida

Mon, 24 May 2021 Source: BBC

Sergio Ramos ba zai buga wa tawagar kwallon kafar Spaniya gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana ba, sakamakon raunin da ya yi faman jinya a kakar 2020/21.

Koci, Luis Enrique ya gayyaci Aymeric Laporte mai tsaron baya maimakon Ramos, wanda a cikin watan nan ya zabi komawa buga wa Spaniya tamauala maimakon Faransa.

Ramos yana cikin 'yan wasan tawagar Spaniya da suka lashe manyan kofi uku tsakanin 2008 zuwa 2012 tun daga lokacin ya zama kashin baya a Spaniya da Real Madrid.

A kakar bana ne Ramos ya doke tarihin da golan Italiya keda shi na yawan buga wa tawagar kwallon kafar Italiya wasa 177.

An nada Ramos mai shekara 35 kyaftin din Spaniya karkashin Luis Enrique cikin watan Maris a wasan neman shiga gasar kofin duniya da Girka da kuma Kosovo, wanda ya yi rauni ya koma Real Madrid jinya.

Wasa 21 kacal Ramos ya buga a kakar bana a dukkan fafatawa, bayan da bai yi karawa 31 ba, kuma Enrique bai gayyaci dan wasan Real Madrid ko daya tawagar Spaniya ba.

Tun a kakar 2020 ya kamata a buga gasar cin kofin nahiyar Turai, amma cutar koron ta kai tsaikon da aka dage wasannin zuwa watan Yuni da za a karkare a Yulin 2021.

'Yan wasan da aka gayyata tawagar Spaniya domin buga gasar nahiyar Turai ta bana:

Unai Simon (Athletic Bilbo) da David De Gea (Manchester United) da Robert Sanchez (Brighton and Hove Albion) da Jose Gaya (Valencia) da Jordi Alba (Barcelona) da Pau Torres (Villarreal) da Aymeric Laporte (Manchester City) da Eric Garcia (Manchester City) da Diego Llorente (Leeds United) da Cesar Azpilicueta (Chelsea) da Marcos Llorente (Atletico Madrid) da kuma Sergio Busquest (Barcelona)

Sauran sun hada da Rodri (Manchester City) da Pedri (Barcelona) da Thiago Alcantara (Liverpool) da Koke (Atletico Madrid) da Fabian Ruiz (Napoli) da Dani Olmo (RB Leipzig) da Mikel Oyarzabal (Real Sociedad) da Alvaro Morata (Juventus) da Gerard Moreno (Villarreal) da Ferran Torres (Manchester City) da Adama Traore (Wolves) da kuma Pablo Sarabia (Paris Saint-Germain).

Source: BBC