Menu

Sunday Igboho: Mutumin da ya kori Fulani daga kudu ya fitar da Yarabawa daga Najeriya

 116637435  116638941 Igh Sunday Igboho

Fri, 19 Mar 2021 Source: BBC

Mutumin nan da ke ikirarin fafutukar kare hakkin Yarabawa, Sunday Igboho, ya ce kabilar Yarbawa za ta balle daga Najeriya saboda rashin adalcin da ake yi mata.

Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a birnin Ibadan da ke kudu maso yammacin Najeriya.

A cewarsa, sun dauki matakin ballewa daga Najeriya ne sakamakon kashe-kashen da makiyaya suke yi wa Yarbawa a jihohin kudu maso yammacin kasar.

Ya yi kira ga dukkan Yarbawa su amince da matakan da shugaban kungiyar kafa kasar Yarbawa ta Nigerian Indigenous National Alliance for Self-determination, Farfesa Banji Akintoye yake dauka na tabbatar da kasar Yarbawa mai cin gashin kanta.

"Abin da muke so shi ne samun 'yancin Yarbawa, kuma babu wanda zai iya tsangwamar babanmu, Akintoye. Idan wani jami'in hukumar tsaro ta farin kaya ko 'yan sanda suka yi yunkurin kama babanmu, za mu mayar da martani. Wannan tsangwama ta isa haka," in ji shi.

A kwanakin baya, Sunday Igboho ya jagoranci wasu masu ikirarin kare hakkin Yarbawa inda suka rika korar Fulani makiyaya daga jihohin kudu maso yammacin Najeriya.

Ya zargi Fulanin da ke yankin da kitsa garkuwa da mutane da kashe-kashe da kuma wasu laifuka da ke faruwa a yankin.

Hakan ya janyo kakkausan martani daga hukumomin kasar da kuma mazauna arewacin kasar.

Hasalima a watan Janairun da ya wuce, mai magana da yawun shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa Babban Sifeton Ƴan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayar da umarni a kamo Sunday Igboho.

A cewarsa, babban jami'in 'yan sandan ya ba da umarnin ne ga kwamishinar ƴan sandan jihar Oyo, Mrs Ngozi Onadeko, inda ya ce ya kai masa shi Abuja.

Sai dai har yanzu ba a kama shi ba kuma ana ganinsa yana yawo a bainar jama'a.

Wasu masu sharhi na ganin Sunday Igboho yana yin irin wadannan kalaman da ake gani na raba kawunan 'yan kasar ne bisa goyon bayan wasu 'yan siyasa da ke ganin ba za su kai labari ba a zaben 2023.

Wane ne Sunday Adeyemo?

An haife shi a 1972 a Igboho da ke Jihar Oyo

Yana sana'ar sayar da motoci sabbi da kuma waɗanda aka yau

Makaniken babur ne lokacin da yake matashi

Yana da gidauniya mai sunansa da ke tallafa wa mabuƙata

Source: BBC