Menu

Sunday Oliseh na fatan sake yin aikin kocin kwallon kafa nan gaba

 118789447 Oliseh Getty 864688226 Sunday Oliseh, tsohon kocin tawagar Najeriya

Fri, 4 Jun 2021 Source: BBC

Tsohon kyaftin din Najeriya, Sunday Oliseh na son ci gaba da horar da tamaula a wata kungiya a Belgium, amma bai fitar da tsammanin karbi aiki daga waje ba.

Mai shekara 46 na zaune baya aiki tun bayan da ya bar kungiyar kwallon kafa ta Fortuna Sittard ta Netherlands a Fabrairun 2018.

Tun bayan da Oliseh ya ajiye aikin horar da Super Eagles, ya zabi yin aiki a Belgium, kan wasu dalilai na kashin kansa.

''Yadda nake kaunar koci a Belgium wani sirri ne a tare dani, saboda ina son na zauna kusa da iyalai na,'' kamar yadda Oliseh ya sanar da BBC.

''Zama kusa da iyalina abu ne mai mahimmaci, amma kan sana'ata, idan na samu aiki da wata kungiya a waje zan iya karba.

''Zan amince da kungiyar da za ta amince mu tattauna kan yadda zan rinka samun lokacin ziyara Belgium da gudanar da aiki a wata kasar.''

Wanda ya lashe kofin nahiyar Afirka a 1994, ya fara taka leda a Julius Betrger a Najeriya, daga baya ya koma Turai a kungiyar RFC Liege ta Belgium da Reggiana da kuma FC Koln ta Jamus.

Oliseh wanda ya lashe lambar zinare a gasar Olympic da Najeriya a 1996 ya kuma buga tamaula a Ajax daga 1997 zuwa 1999, inda ya lashe kofin gasar Netherlands da kofin kalubalen kasar biyu.

Yana daga cikin fitattun 'yan wasan Najeriya da suka taka rawar gani a Super Ealges da ake cewa ba kamarsu tare da Jay-Jay Okocha da Nwankwo Kanu da Daniel Amokachi da kuma Finidi George.

Oliseh wanda ya yi wasa a Juventus da Borussia Dortmund da VFL Bochum da kuma Genk, ya buga wa tawagar kwallon kafar Najeriya karawa 63.

Ya buga wa Super Eagles gasar cin kofin nahiyar Afirka biyu da kofin duniya, daga baya ya yi ritaya daga yi wa Najeriya wasa a 2002.

A Julin 2015, Oliseh ya zama tsohon dan wasan Najeria na hudu daga ajin 'yan wasan 1994 na Super Eagles da ya yi kocin tawagar, bayan Austin Eguavoen da Samson Siasia da kuma Stephen Keshi.

Source: BBC