Menu

Tambayoyin da ƴan Najeriya ke so Majalisar Dattawa ta yi wa hafsoshin tsaro

Major General Ibrahim Attahiru Ibrahim Attahiru, Shugaban hafsan sojojin Najeriya

Thu, 6 May 2021 Source: BBC

Ƴan Najeriya sun bayyana irin tambayoyin da ya kamata ƴan majalisa su yi wa manyan hafsoshin tsaron ƙasar kan sha'anin tsaro idan sun bayyana gabansu.

Ranar Talata ne Majalisar dattawan Najeriya ta aike wa hafsoshin tsaron Najeriya da gayyata dangane da matsalar tsaro da ta addabi ƙasar.

Wannan ya biyo bayanan da wani dan majalisar jihar Neja Honorabul Sani Musa ya bayar a makon jiya inda ya ce kusan ƙauyuka 42 ne ke hannun 'ƴan bindiga a mazabar da yake wakilta kaɗai.

Majalisar ta ce wannan batu ya yi matuƙar tayar mata hankali shi ya sa ta buƙaci ganin hafsoshin tsaron don tattauna yadda za a samo hanya mai ɗorewa ta samar zaman lafiya.

Haka kuma, majalisar ta ce ta gayyaci sauran hukumomin tsaro kamar Jami'an tsaro na farin kaya da Civil Defence da dai sauransu saboda lamarin ya kai matsayin da sai kowa ya sa hannu a ciki.

Wannan batu ya ja hankalin ƴan Najeriya matuƙa kuma sun bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta.

Wannan ne ya sa muka jefa tambaya ga masu bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta cewa: Me ya kamata su yi domin kawo karshen matsalar tsaro a kasar?

Mafi yawan tambayoyin sun fi mayar da hankali kan yadda matsalar tsaron ke ƙara ta'azzara.



Balarabe Urwatu a shafinsa @Urwatu ya yi tsokaci cewa: Ina so hafsoshin tsaron su bayyana wa majalisar abubuwan da suke buƙata don shawo kan matsalolin na tsaro sannan su faɗi abin da suka yi da kayan aikin da aka samar a baya.

Shi kuwa wani mai amfani da shafin Twitter Abubakar B Kuni cewa ya yi bai kamata a ce majalisar ta gayyaci hafsoshin tsaro kaɗai ba, Shugaba Muhammadu Buhari ma ya kamata ya je gaban majalisar don yin bayani dangane da matsalar tsaron ƙasar.

Auwalu Aliyu ɗan Fulani ya bukai a tambayi shugabannin tsaron dalilin da ya sa ba a ganin jami'an tsaro idan an sanar da su an kawo hari.

Wata mai amfani da shafin Facebook Maman Islam ta ce matsalar ba a jami'an tsaro ba ne, ya kamata gwamnati ta samar da kayan aiki na zamani ta damƙa wa sojoji sannan a inganta ƙudin da ake biyansu.

Ta ce wannan zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya.

Isah Isah Kwafsi Asarara, mai amfani da shafin Facebook ya ce yana ganin cewa rashin haɗin kai tsakanin hafsoshin tsaron ne ke ƙara taɓarɓara lamarin.

Ya ce da a ce za su riƙa musayar bayanai da juna da sun gano abubuwa da dama game da yadda ƴan bindiga ke hulɗa.

Ba wannan ne karon farko da majalisa ta ke gayyatar hafsohsin tsaro don amsa tambayoyi dangane da batun tsaro ba, amma wannan ne karon farko da waɗannan hafsoshin tsaron za su je gaban majalisar.

A watan Janairu ne Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa sabbin hafsoshin tsaro a ƙasar da ta daɗe tana fama da matsalolin fashin daji da garkuwa da mutane don kuɗin fansa da kashe-kashe.

Sai dai naɗa sabbin hafsoshin bai sauya komai ba don kuwa an ci gaba da fuskantar waɗannan matsalolin.

Lamarin tsaro sai ƙara ta'azzara yake saboda a baya rashin tsaro ya fi ƙamari a yankin arewacin ƙasar amma a watannin baya-bayan nan, yankin kudu ma na fuskantar matsaloli na kisan ƴan sanda da kai hari ofisohin ƴan sandan da sace makamansu da kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

A ranar Alhamis ne ake sa ran hafsoshin tsaron za su gurfana a gaban majalisar dattawan.

Source: BBC